Yadda Budurwa Mai Shekaru 22 Ta Fada Soyayyar Tsohon Mai Shekaru 88 Har Ta Samu Juna Biyu

Yadda Budurwa Mai Shekaru 22 Ta Fada Soyayyar Tsohon Mai Shekaru 88 Har Ta Samu Juna Biyu

  • Duk da cewar akwai tazarar shekaru 66 tsakanin Chibalonza da Kasher Alphonse, hakan bai hana su fadawa soyayya ba
  • A yanzu haka, matashiyar mai shekaru 22 tana dauke da juna biyu inda ma’auratan za su haifi dansu na farko a tare
  • Sai dai Alphonse na fargabar cewa yaransa wadanda suka girme ma kishiyar uwar tasu za su azabtar da ita da zaran ya fadi ya mutu

Chibalonza ta kasance matashiya yar shekaru 22, amma kuma sai ta fada a tarkon soyayya da tsohon da ya isa yin jika da ita, wato Kasher Alphonse mai shekaru 88.

Mutumin ya fada ma Afrimax English cewa sun kasance suna son juna kuma sun fahimci junansu duk da banbancin shekaru 66 da ke tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Lokaci Yayi: Bayan Shekaru 11 ana Zuba Soyayya har da Haihuwar Yara 2, Masoyan Sun Angwance

Masoya
Yadda Budurwa Mai Shekaru 22 Ta Fada Soyayyar Tsohon Mai Shekaru 88 Har Ta Samu Juna Biyu Hoto: Afrimax Media.
Asali: UGC

Uwargidar Alphonse ta farko ta mutu shekaru biyu da suka gabata

A cewar masoyan wadanda suka shafe tsawon shekaru biyu tare, sun fada a tarkon soyayya da zuciyoyinsu ne amma ba wai da shekarunsu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alphonse ya auri matarsa ta farko a 1954 lokacin yana da shekaru 24 a duniya sannan sun haifi yara bakwai a tare.

Bayan shekaru da dama da suka dauka tare, uwargidar tasa ta rasu saboda tsufa, inda ta barshi da kewa shi kadai domin dukkanin yaran sun girma kuma sun bar gidan.

Saboda tsufa, Alphonse yana shan fama wajen yiwa kansa abubuwa da dama, don haka ya nemi taimako.

Basu yi aure ba a hukumance

Ya yi dacen haduwa da Chibalonza, wacce take da shekaru 20 a wancan lokacin amma ta yarda ta zamo matarsa.

“Ba mu yi aure ba a hukumance amma mun yi auren gargajiya. Harma na kaiwa yan uwanta katan din lemu da akuya,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Soyayya gamon jini: Tsoho mai shekaru 93 yayi wuff da budurwarsa mai shekaru 88

Dattijon ya bayyana cewa bai san yadda yaransa za su kula da kishiyar mahaifiyar tasu ba idan ya fadi ya mutu, amma ya damu sosai a kan haka.

Danasaninsa kawai shine cewa bai da kudin siyan wani filin a wani waje don amaryarsa ta samu gidanta ba gidan iyalinsa na farko ba.

Chibalonza ta yi nauyi

Alphonse na shirin yin bikin aure idan matarsa wacce ke dauke da juna biyu a yanzu ta haihu.

Mutane da dama da ke sane da shirye-shiryen na mamaki saboda yaran Alphonse sun girme ma kishiyar mahaifiyarsu nesa ba kusa ba, dansa na fari shekarunsa 66 yayin da autansa ke da shekaru 50.

Yanayin Alphonse sun nuna shi talaka ne, amma ya ce yana da rufin asiri sosai a zamanin kuruciyarsa harma yana da shagon daukar katan-katan din lemuka.

Sai dai kuma kasuwancin ya rufe ne bayan wasu ‘yan fashi da suka addabi shagonsa lamarin da ya sa ya kasa ci gaba da gudana.

Kara karanta wannan

Jarumar Mata: Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Zukekiyar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Aminu Bayero Za Ta Shiga Daga Ciki

A wani labarin, Ruqayya Aminu Bayero, kyakkyawar diyar sarkin Kano, Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, na shirin amarcewa da angonta.

Za a kulla aure tsakanin Rukayya da angonta Amir Kibiya a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba mai kamawa a fadar mai martaba Sarkin Kano.

Tuni katin gayyatar auren ya bayyana a shafukan soshiyal midiya kuma shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng