Tsohon Sarkin Kano Sanusi Ya Bukaci Matasa Su Daina Fita Waje, Su Tsaya a Najeriya
- An yi kira ga matasan Najeriya a duk fadin kasar nan da su zauna daram domin bunkasa hazakar da Allah ya ba su maimakon barin kasar nan zuwa neman dama a waje
- Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ne ya yi wannan kira ga matasa a ranar Lahadi, 7 ga watan Agusta
- Sanusi ya kuma roki matasa a Najeriya da su tabbatar shugabanni, musamman masu rike da mukaman gwamnati sun yi aikinsu
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Najeriya - Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu, ya yi kira ga matasan Najeriya da su daina barin kasar nan domin neman dama a kasashen waje, rahoton TheCable.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Sanusi ya yi wannan kira ne ga matasan yayin da yake jawabi a ranar Lahadi a wani wasan kwaikwayo mai taken 'A Truth in Time'
Taron wanda ya naqalto rayuwa da gogewar tsohon sarkin, Ahmed Yerima, farfesa ne na fannin wasan kwaikwayo a Jami’ar Redeemer, ya rubuta shi, wanda Duke of Shomolu Productions ya shirya.
A cewar tsohon sarkin na gargajiya, akwai bukatar matasa a fadin kasar nan su fara bunkasa fasaharsu a nan cikin gida.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kuma bukaci matasa a Najeriya da su yi kokarin ganin sun yi wa shugabanni da masu rike da mukaman gwamnati jan ido wajen tabbatarwa sun yi aikin da aka daura musu.
A kalamansa:
“Gare ku matasa, kada ku ji tsoro. Wannan ita ce kasarku. Wannar ita ce makomarku. Ku rike ta. Ku yi aiki don ita. Ku gina ta. Kada ku bari kowa ya ce ku gudu saboda kuna da digiri."
Yiwa shugabannin Najeriya jan ido
Jaridar The Punch ta rawaito cewa Sanusi ya ce an gargade shi har ma da zarge shi da sukar gwamnati a bainar jama'a.
Da yake koka cewa a halin yanzu kasar na fuskantar mawuyacin hali, Sanusi ya yi gargadin cewa Najeriya ba za ta ci gaba ba matukar dai matasa basu karbi mulkin kasarsu ba.
Ya kara da cewa:
"Suna tsammanin sun sami 'yancin fada muku lokacin da ya kamata ku yi magana da lokacin da bai kamata ku yi magana ba.
"Suna tsammanin sun sami 'yancin sarrafa ra'ayoyinku kuma ba za a iya sukarsu ba. Gaskiyar ita ce ba su da wannan 'yancin."
Duk da tsige ni, ba zan kame baki na game da Najeriya, tsigaggen sarkin Kano Sanusi
A wani labarin, tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana kwarin gwiwar ci gaba da magana kan karewa da sake gina fasalin Najeriya.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Sarkin ya ce galibin maganganunsa da suka jawo masa matsaloli a baya sun zo kuma mutane sun gani.
Tsohon Sarkin wanda yanzu shi ne Khalifan Darikar Tijjaniyyah ta Najeriya ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Asabar 6 ga watan Agusta a wani wasan kwaikwayo mai taken “Emir Sanusi: Truth in Time” da aka shirya.
Asali: Legit.ng