A Ci Gaba da Yi: Dalibin Jami’a Ya Kama Sana’a, Ya Ce ASUU Su Tabbata Suna Yaji Kawai

A Ci Gaba da Yi: Dalibin Jami’a Ya Kama Sana’a, Ya Ce ASUU Su Tabbata Suna Yaji Kawai

  • Wani dalibi dan aji 3 a fannin lissafi a Jami’ar Bayero ta Kano, ya koka kan yadda shaidarsa ta ta makaranta za ta daina amfani, kuma bai kammala karatun nasa ba
  • A wata tattaunawa, dalibin ya bayyana yadda ya fara sana'a a shekarar 2020, kuma yake fatan karfafa ta a yanzu
  • Dalibai da dama a Najeriya sun kama sabbin sana'o'i sakamakon jarrabawar da ASUU ta jefa su na zaman gida

Jihar Kano - Abdulhadi Dankama ya samu shiga sashen ilmin lissafi a jami'ar Bayero ta jihar Kano domin yin digirinsa na farko.

Ya kamata Dankama ya kammala digirinsa a yanzu idan da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta fara ba kan rashin jituwa da gwamnatin tarayya bata shafe shi ba.

Za ku yi tunanin Dankama wanda a yanzu yana aji 3 zai kosa ya koma makaranta domin ya gaggauta kammala karatunsa.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Yadda dalibin jami'a ya kama sana'ar siyar da shayi don yakar zaman kashe wando

Matashi ya kama sana'a, ya ce bai damu ba ASUU idan suka ki janye yaji
A ci gaba da yi: Daliban jami'a ya kama sana'a, ya ce ASUU su tabbata suna yaji kawai | Hoto: Abdulhadi Dankama
Asali: UGC

Sai dai ga dukkan alamu tunanin matashin ya kau, ya bar batun neman digirin da yake yi tun da ya ce bai damu ba ko da ASUU sun ki amincewa a bude jami'o'i.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yana da wani shiri na daban a rayuwa

A farkon barkewar cutar ta Korona a 2020, Dankama ya fara kasuwancin siyar da 'ya'yan itace. Ya fara ta ne ta wata hanya ta musamman domin kuwa shi har ta yanar gizo yana iya siyar da hajarsa.

Lokacin da batun Korona ya lafa, kuma aka koma makaranta, Dankama bai daina siyar da 'ya'yan itace ba. Maimakon haka, ya kafa kasuwa mai karfi.

Ya tuna yadda ya fara:

"Na fara siyar da 'ya'yan itatuwa a lokacin kulle-kulle Korona. A cikin watan Ramadan, mutane suna gida saboda cutar, ba sa zuwa ko'ina. Don haka, lokacin ne tunanin ya zo min.

Kara karanta wannan

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

"Na yi tunanin tun watan Ramadana ne kuma mutane suna bukatar 'ya'yan itatuwa, me zai hana in gwada siyarwa ta yanar gizo?"

Ya ce kasuwancin ’ya’yan itacen da ya fara ta yanar gizo ya bunkasa a lokacin barkewar cutar tun a lokacin yakan kai wa abokan cinikinsa hajarsa har gida kyauta.

Yace:

"Na fara ta yanar gizo ne saboda ban taba ganin wanda ya gwada hakan ba. Yawancin abokaina ba su yarda da tunanin kasuwancin ba, amma duk da haka na je fara, suna kallon kasuwancin a matsayin karami."

Yajin aikin ASUU

Babu shakka, lokacin da Legit.ng ta zanta da Dankama, batutuwansa sun tabbata irin kaunar da yake wa sana'ar tasa da ya fara.

Yana matukar son kasuwancin 'ya'yan itatuwa kuma yana shirin fadada jari. Ba don yajin aikin ASUU ba, ta tuni ya kamma ya fice daga jami’ar Bayero ya maida hankali kan harkokinsa na sana'a kamar yadda ya ce yana shirin bude sabbin rassa a jihar.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wani Mutum Ya Yanke Jiki Ya Fadi Sumamme Bayan Ya Rasa N200k Da Ya Ranta A Wajen Buga Caca

Hakan bai samu ba. kasancewar ASUU ta fara yajin aiki, lamarin da ya shafi dalibai da dama ciki har da Dankama.

Amma da alama Dankama bai damu da abin da ke faruwa na yaji ba domin ya shaida wa Legit.ng cewa ya kamata ma a ci gaba da yajin aikin domin ya samu ya kammala shirya kasuwancinsa.

Yajin aikin ASUU: Dalibin aji 2 a jami'a ya koma sayar da shayi a Kano

A wani labarin, wani dalibin aji biyu na Jami’ar Yusuf Maitama Sule da yajin aiki ASUU ya shafa ya kama wata sana’ar sayar da “Shayi” a garin Dawakin Dakata da ke karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano domin kaucewa zaman banza.

Dalibin mai karanta Tarihi da Hulda da Kasashen Duniya wanda ya bayyana sunansa da Yusuf Auwal Barkum, a wata hira da ya yi da Sahelian Times, ya ce ya yi nadamar rashin kama sana’ar tun da farko.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

Teburin shayi dai kasuwanci ne na gida inda ake sayar da dafaffiyar taliya, kwai, shayi da burodi, galibi a fili da ke da karamin shago da benci, teburi da kujeru a zagaye dasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.