Yan Bindiga Da Yawa Sun Mutu Yayin Arangama Da Jami'an Tsaro a Jihar Filato
- Dakarun Operation Safe Haven da haɗin guiwar yan Banga sun samu nasarar ta da sansanin yan bindiga biyu a jihar Filato
- Yayin samamen a yankin ƙaramar hukumar Wasu, jami'an tsaron sun halaka yan ta'adda da dama sun kwato kauyuka biyu
- Wannan nasara na zuwa ne yayin da hukumomin tsaro a Najeriya ke cigaba da kokarin dawo da zaman lafiya
Plateau - Aƙalla yan bindiga Takwas ne suka sheƙa barzahu yayin gwabzawa da Jami'an tsaro a ƙauyen Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Wase, jihar Filato.
Daily Trust ta ce an samu wannan nasara ne a wani samamen haɗin guiwar Sojojin Operation Safe Haven, rundunar gamayyar jami'an tsaro da ke aikin tabbatar da tsaro a jihar, da yan Banga.
Gamayyar jami'an tsaron na aikin kai samame maɓoyar yan bindigan ne da nufin kakkaɓe yan ta'adda baki ɗaya daga yankin ƙaramar hukumar Wase.
Wannan nasarar ta baya-bayan nan ta zo ne mako biyu bayan aika yan bindiga 16 lahira a kauyen Bangalala, duk a wannan ƙaramar hukumar ta Wase, jihar Filato.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai magana da yawun dakarun OPSH, Manjo Ishaku Takwa, wanda ya tabbatar da nasarar ga yan jarida, ya ce, "Yan bindiga Takwas sun sheƙa barzahu yayin samame a yankin."
Kakakin ya ƙara da cewa sun fara aikin kai samamen ne ranar Asabar kuma ba zasu gajiya ba zasu cigaba da haka don dawo da zaman lafiya, kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito.
Shin dagaske jami'an tsaro sun samu nasarar?
Wani mazaunin Wase, Abdullahi Usman, wanda ya tabbatar da lamarin ya ce kauyuka biyu, Zurak da Yaddi Lawan, waɗan da yan bindigan suka kwace suka maida sansanin su, sun koma hannun jami'an tsaro.
A kalamansa ya ce:
"An kashe wasu yan bindiga yayin da jami'an tsaro ke cigaba da bin sawun sauran da suka tsere. Samamen na haɗin guiwa ne, Sojoji da Yan Bijilanti kuma sun yi nasara. ina da yaƙinin zasu cigaba yau."
A wani labarin kuma Jami'an NDLEA sun kama wani Soja mai Ritaya ɗan Shekara 90 dake kaiwa yan bindiga ƙwayoyi
Hukumar NDLEA ta kama wani tsohon Soja ɗan shekara 90 a duniya da ke aikin kaiwa yan bindiya kwayoyi a Sakkwato.
Mai magana da yawun hukumar ya ce mutumin ya shiga hannu ne a kauyen Mailalle, ƙaramar hukumar Sabon Birni.
Asali: Legit.ng