Bidiyo: Mai siyar da tsire ya zama ɗan gaye bayan kamfani sun ɗauke shi talla

Bidiyo: Mai siyar da tsire ya zama ɗan gaye bayan kamfani sun ɗauke shi talla

  • Wani mutumi 'dan Najeriya mai suna Alhassan Ibrahim, 'dan asalin jihar Kano mai siyar da tsire a Ibadan ya bayyana yadda rayuwarsa ta canza
  • Kafin ya fara yi wa wani kamfani talla, sai da aka wanke tare da gyara mutumin, lamarin da ya sauya masa kamanni gaba daya
  • Jama'a sun yi martani kan bidiyon inda wasu ke cewa babu namiji mummuna, kudi na iya sauya shi zuwa zukeken matashi

Wani matashi 'dan Najeriya mai suna Alhassan Ibrahim, 'dan asalin jihar Kano dake siyar da tsire a Ibadan, ya samu sauyin rayuwa baki daya a lokaci daya.

A wani gajeren bidiyo da @onlyinnigeria suka wallafa a Instagram, mutumin yace yana da mata, 'ya'ya da 'yan uwa.

Hausa Man
Bidiyo: Mai siyar da tsire ya zama ɗan gaye bayan kamfani sun ɗauke shi talla. Hoto dga @onlyinnigeria
Asali: Instagram

Jama'a da yawa sun ce gyaran da mutumin ya samu ya canza shi kwata-kwata.

Kara karanta wannan

Ango ya rasu bayan kwana 12 da aure, bidiyon aurensu da kyakyawar amaryarsa ya taɓa zukata

A farkon bidiyon, an gan shi yana siyar da tsirensa yayin da bidiyo na biyu ya nuna yadda ake yi masa askin 'yan gayu a wurin mai askin zamani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani kwararren mai askin zamani ne ya gyara masa gashin gemunsa. Bayan askin, ya canza kamanni sosai.

A yayin daukar hotunan tallan da zai yi wa wani kamfani, ya karkace tamkar kwararre. Ya bayyana cewa, kamfanin da ya bai wa dama sun gwangwaje shi da kayayyakinsu.

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da aka yi kan bidiyon

Ga wasu daga ciki:

aria_loveth tace: "Kowa yana da kyau, kudi ne ke nakasta mutane."
Yongfaces yace: "Wannan yasa ni kuka, a gaskiya dabara ce mai kyau kuma ya matukar dacewa da kamfanin da yake wa talla."
Ibhafidon_miracle yace: "Kai, kyakyawa ne. Ya yi kama da bakaken Amurka masu kwallon kwando."

Kara karanta wannan

Arangamar masoya: Matashin Najeriya ya hadu da baturiyar da suka yi shekaru 2 suna soyewa a yanar gizo

Iamscat tace: "Ina fatan an biya shi da ababen arziki. Ya dogara da tsawon lokacin da aka dauka ana tallar ya kamata ya samu kyautuka kamar kowanne mai talla."
aishaachonu tace: "Kuma yayi kyau, babu abinda gyara ba zai yi ba!"
Opejodu yace: "Wadannan hotunan sun yi wuta."

Osogbo zuwa Legas a kasa: 'Dan Najeriya ya fara tattakin karrama MKO Abiola

A wani labari na daban, wani 'dan Najeriya mai suna Innocent C. Kwantagora ya daukowa kansa babban aiki yayin da yace zai tattaka tun daga Osogbo a jihar Osun har zuwa jihar Legas.

Duk da bai bada takamaiman ranar da zai isa Legas ba, bayanai da Legit.ng ta tattaro sun bayyana cewa zai ratsa ta Ibadan, Abeokuta sannan ya dire a jihar Legas.

Jama'ar da suka san da batun tattakin sun bayyana cewa, mutumin yana son yin amfani da wannan tafiyar ne wurin wayarwa jama'a da kai a fannin lafiyar kwakwalwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, a Mimbarin Coci yana ihun 'Ku Yabi Ubangiji' ya janyo cece-kuce

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng