NECO: Za a Fitar da Sakamakon Jarabwar SSCE Nan da Kwanaki 45
- Rajistaren Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Wushishi, ya yi alkawarin fitar da sakamakon Jarrabawar NECO Nan da Kwanaki 45
- Farfesa Ibrahim Wushishi ya kai ziyarar sa ido a wasu cibiyoyin gudanar da jarabawar NECO a jihar Legas
- Wushishi ya ce Hukumar NECO ta hada kai da Jam'iyyar Tsaro dan sa ido kan kayar jarabawar da aka tura wuraren dake fuskantar matsalar tsaro
Jihar Legas - Rajistaren Hukumar Shirya Jarrabawa ta Kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Wushishi, ya yi alkawarin cewa za a fitar da sakamakon Jarrabawar Sakandare ta 2022 (SSCE) nan da kwanaki 45 bayan kammala jarrabawar karshe. Rahoton Daily Trust
Wushishi ya bayyana haka ne a lokacin da yaje ziyarr sa ido kan yadda jarabawar SSCE ke gudana a wasu cibiyoyi a Legas.
Ana sa ran kammala jarrabawar da aka fara a watan Yuni a ranar 12 ga watan Agusta.
Wushishi yace suna kan lamarin kuma suna ba da tabbacin cewa za a fitar da sakamakon jarabawar da ke gudana nan da kwanaki 45 bayan kammala na karshe
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kuma bayyana cewa dalibai 1.29m suke zana jarabawar da ake yi.
Da yake tsokaci kan rashin tsaro a wasu sassan kasar, shugaban NECO ya bayyana cewa an yi isassun shirye-shirye da jami’an tsaro don sa ido akan kayan jarabawar.
Buhari, Tinubu, IGP, Oyetola, Da Sauran Su Sun yi Jimamin Mutuwar Tafa Balogun
A wani labari kuma, A jiya ne shugaba Buhari ya mika gaisuwar ta’aziyyar sa ga rundunar yan sandan Najeriya, yan uwa da abokan arziki na tsohon sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya Tafa Balogun da ya rasu a ranar Alhamis. Rahoton The Nation
Shima dan takarar shugabankasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, Sufeto Janar Usman Baba da gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola sun mika na su sakon ta’aziyar.
Asali: Legit.ng