Osogbo zuwa Legas a kasa: 'Dan Najeriya ya fara tattakin karrama MKO Abiola

Osogbo zuwa Legas a kasa: 'Dan Najeriya ya fara tattakin karrama MKO Abiola

  • Wani matashi mai suna Innocent C. Kwantagora ya fara tattakin tarihi a kafa inda yace zai tattaka daga Osogbo zuwa Lagos
  • Kamar yadda bayanai da Legit.ng ta tattaro suka bayyana, mutumin yace makasudin tafiyarsa shine karrama MKO Abiola
  • Bayanai sun tabbatar da cewa mutumin zai yi amfani da wannan tattakin wurin wayar da kan mutane a fannin lafiyar kwakwalwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani 'dan Najeriya mai suna Innocent C. Kwantagora ya daukowa kansa babban aiki yayin da yace zai tattaka tun daga Osogbo a jihar Osun har zuwa jihar Legas.

Duk da bai bada takamaiman ranar da zai isa Legas ba, bayanai da Legit.ng ta tattaro sun bayyana cewa zai ratsa ta Ibadan, Abeokuta sannan ya dire a jihar Legas.

Madugu
Osogbo zuwa Legas a kasa: 'Dan Najeriya ya fara tattakin karrama MKO Abiola
Asali: Original

Jama'ar da suka san da batun tattakin sun bayyana cewa, mutumin yana son yin amfani da wannan tafiyar ne wurin wayarwa jama'a da kai a fannin lafiyar kwakwalwa a Najeriya.

Kara karanta wannan

An Gindaya Sharuda Kafin a Cigaba da Karatu a Kwalejin da aka Kashe Deborah

An kara da cewa, zai yi amfani da wannan tafiyar ne domin karrama MKO Abiola, wanda ya lashe zaben ranar 12 ga watan Yunin 1993 na shugabancin kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiyar Legit.ng tace:

"Yana tattaki daga Osogbo zuwa Ibadan, zai ratsa ta Abeokuta kuma ya isa Legas domin wayar da kan mutane kan lafiyar kwakwalwa da karrama MKO Abiola."

Ba a san ranar isarsa ba

Majiyar ta kara da cewa, mutumin na son kamfanonin sadarwa su samar da layukan da ba a cajar kudi ga mutane dake fama da matsalar kwakwalwa.

Sai dai, ranar da mutumin zai isa Legas ne ba a sani ba, amma tuni ya fara tafiyar. Sannan ba a san lokacin da zai dauka domin kammala doguwar tafiyar ba.

Ina zan gan shi?: Ahmed Musa ya shirya taimakon tsohon zakaran Olympic dake cike kwararon titi a Legas

Kara karanta wannan

2023: Ana Kokarin Kawo Karshen Rikicin Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Zauna da Wike

A wani labari na daban, Kyaftin din kungiyar wasan kwallon kafa ta Najeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa, yana son taimakawa tsohon zakaran wasannin Olympic, Bassey Etim, wanda aka gani a yankin Ajah ta jihar Legas yana cike kwazazzaban kan titi.

A baya ana kiran zakaran da 'Iron bar', an gan shi a wani sashin titin Ado/Badore a jihar Legas.

Mawakin Najeriya, Oc Cares, ya bayyana yadda ya ga Bassey na aikin taimakon al'umma a tituna na tsawon lokaci, lamarin da yasa ya neme shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng