Kano: Sarkin Bichi ya shirya taron addu'ar Allah ya kawo karshen rashin tsaro a Najeriya
- Sarkin Bichi ya tara malamai a yau Juma'a domin gudanar da taron addu'ar zaman lafiya yankin Arewa
- Taron ya kuma hada rokon Allah ya wanzar da zaman lafiya a kasar kafin zaben 2023 mai zuwa nan kusa
- Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro a daidai lokacin da zaben 2023 ke kara gabatowa nan ba da jimawa ba
Jihar Kano - Mai martaba Sarkin Bichi da ke Kano, Alhaji Nasiru Ado Bayero, ya shirya taron addu’a domin neman taimakon Allah kan matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan, musamman a Arewa.
An gudanar da taron addu’ar ne a babban masallacin Bichi a ranar Juma’a, inda ya samu halartar mai martaba sarki da hakimai da malamai da kuma al’ummar masarautar, Daily Trust ra ruwaito.
Babban limamin masarautar Bichi, Khalifa Lawal Abubakar Bichi ne ya jagoranci zaman tare da karatun Alkur’ani mai girma, sannan ya yi addu’o’i ga shugabanni da sauran al’ummar kasar nan.
Yayin da yake addu’ar kawo karshen kalubalen tsaro, limamin ya kuma yi addu’ar samun albarkar noma, tare da neman taimakon Allah wajen tabbatar da zabe cikin lumana, adalci, gaskiya da kuma sahihanci a 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar limamin:
“Muna bukatar mu tuba ga Allah da neman gafararsa. Duk wadannan suna faruwa ne sakamakon dabi'unmu da munanan ayyukanmu. Allah ya gafarta mana baki daya.”
Ya zama wajibi a yi addu'o'i, Farfesa Yusuf Muhammad Sabo
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala addu'ar, shugaban karamar hukumar Bichi, Farfesa Yusuf Muhammad Sabo, ya ce taron addu’ar ya zama wajibi duba da irin kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta.
Yayin da babban zaben shekarar 2023 ke kara matsowa, ya bayyana cewa akwai bukatar a rika yin addu’o’i masu yawa domin samun zaman lafiya da shugabanci na gari, rahoton Daily Post.
Ya kuma ce:
"Ya kamata kuma mu yi kokari mu yi addu'a don yin zabe lafiya a 2023."
Zabe za a yi ba 'wuruwuru': Shirin da Buhari ke yi gabanin babban zaben 2023
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi gargadin cewa ba zai bari a yi magudin zabe ko rashin da’a a karkashin kulawarsa ba a zaben 2023 mai zuwa.
Shugaban ya fadi haka ne a wani taron karawa juna sani kan harkokin tsaro na ‘Election Security Management’ wanda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta shirya a Abuja.
Shugaban ya samu wakilcin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), inda ya ba da tabbacin cewa babu wata jam’iyyar siyasa ko wani mutum da zai zo da wargi a lokacin zabe.
Asali: Legit.ng