Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Google Ta Hana IPOB Shiga Dandalin Ta

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Google Ta Hana IPOB Shiga Dandalin Ta

  • Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya roki kamfanin Google da ta hana mambobin kungiyar ‘yan asalin Biafra amfani da dandalinta
  • Alhaji Lai Mohammed ya ce kungiyar ‘yan asalin Biafra IPOB na amfani da Google wajen tada zaune tsaye a Najeriya
  • Google ta ce ta bullo da wani shiri da zai rika bibiyar abubuwan da ke cikin intanet domin dakile masu yada ta’adanci

Abuja - Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a ranar Alhamis ya roki kamfanin Google da ta hana mambobin kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB) damar amfani da dandalinta. Rahoton Daily Trust

Da yake magana jiya a Abuja a lokacin da wata tawagar Google ta ziyarce shi, ya ce:

“haramtattun kungiyar ta’addanci” suna amfani da dandalin wajen ayyukan tada kayar baya da kuma tada zaune tsaye.

Kara karanta wannan

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

Ministan yace yana son Google ta duba yadda za a magance amfani da tashoshi masu zaman kansu na YouTube da haramtattun kungiyoyi ke amfani da shi wajen yada ta’addanci.

Mohammed
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Google Ta Hana IPOB Shiga Dandalin Ta FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mohammed ya ce ‘yan Najeriya na cikin wadanda suka fi yin amfani da kafafen sada zumunta a duniya, inda sama da miliyan 100 ke amfani da intanet.

Ya ce, duk da haka, wadanda ba su da mutunci suna amfani da wadannan kafafan domin yin zagon kasa ga kasar da kuma aikata munanan ayyuka kamar yahoo yahoo.

Darektan Google na yankin Afrika, Charles Murito, ya ce dandalin ya bullo da wani shiri mai suna “Trusted Flaggers” ga ‘yan kasa da aka horar da su wajen bibiyar abubuwan da ke cikin intanet domin dakile masu yada ta’adanci.

Muna Bukatar Shirin Da Zai Daura Mu Sama Da Yan Ta’adda – Osinbajo Ya Fadawa Sojoji

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun harbi shugaban 'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa

A wani labari kuma, Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta dauki matakin da zai sanya tunanin su gaba da ‘yan ta’adda da ke barna a fadin kasar. Rahoton Channels TV

Ya ce kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu da barazanar da ke kunno kai, yana bukatar sojoji da sauran masu ruwa da tsaki su kasance cikin shiri tare da kara kaimi wajen kirkiran makamai a cikin gida

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa