Zukekiyar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Aminu Bayero Za Ta Shiga Daga Ciki

Zukekiyar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Aminu Bayero Za Ta Shiga Daga Ciki

  • A farkon wata mai kamawa jihar Kano za ta yi cikar kwari domin za a yi gagarumin biki na gidan sarauta mai daraja ta daya
  • Alkawari na shirin cika tsakanin diyar Sarkin Kano, Ruqayya Aminu Bayero da angonta Amir kibiya
  • Za a daura auren na sarauta a ranar 2 ga watan Satumban 2022 a fadar mai martaba sarkin Kano da cikin birnin jihar

KanoRuqayya Aminu Bayero, kyakkyawar diyar sarkin Kano, Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero, na shirin amarcewa da angonta.

Za a kulla aure tsakanin Rukayya da angonta Amir Kibiya a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba mai kamawa a fadar mai martaba Sarkin Kano.

Ruqayya Bayero
Zukekiyar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Aminu Bayero Za Ta Shiga Daga Ciki Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

Tuni katin gayyatar auren ya bayyana a shafukan soshiyal midiya kuma shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Shirya Angwancewa Da Kanwar Marigayiyar Budurwarsa Bayan Mako 1 Da Mutuwarta

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matashi Ya Shirya Angwancewa Da Kanwar Marigayiyar Budurwarsa Bayan Mako 1 Da Mutuwarta

A gefe guda, wani matashi dan Najeriya mai suna Sufiyanu Abubakar Salihu na shirin angwancewa da Fatima Ibrahim Kani, kanwar budurwarsa da ta rasu.

Tun farko dai an shirya yin auren Sufiyanu da Rukayya Ibrahim Kani a ranar 12 ga watan Agusta a jihar Bauchi amma sai Allah ya yi mata rasuwa a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli.

Sufiyanu da kansa ya je shafin Twitter a ranar 28 ga watan Yuli inda ya sanar da rasuwar Rukaiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng