Matar Marigayi Alaafin Na Oyo Ta Dawo Daga Saudiyya Kawai Sai Ta Tarar Da Kyautar Mota Daga Wani Bawan Allah

Matar Marigayi Alaafin Na Oyo Ta Dawo Daga Saudiyya Kawai Sai Ta Tarar Da Kyautar Mota Daga Wani Bawan Allah

  • Daya daga cikin matan Marigayi Alaafin na Oyo, Omobolanle, ta shiga sahun miliyoyin Musulmin duniya wajen sauke farali
  • Matashiyar matar ta dawo daga Saudiyya kawai sai ta tarar da kyauta na jiranta
  • Don haka ta je shafin soshiyal midiya don nuna godiyarta ga mai kyautan wanda bata san shi ba
  • Omobolanle ta kara da cewar dawowa gida da tayi ta tarar da kyautar alamu ne da ke nuna Allah ya karbi addu’anta

Sarauniya Omobolanle ta dawo gida daga kasa mai tsarki inda ta sauke farali kawai sai ta tarar da wani tsadadden kyauta yana jiranta.

Matashiyar matar wacce ta kasance daya daga cikin matayen marigayi Alaafin na Oyo ta wallafa wani bidiyo na motar da wani bawan Allah da bata sani bay a ajiye mata.

Kara karanta wannan

Jarumar Mata: Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Omobolanle
Matar Marigayi Alaafin Na Oyo Ta Dawo Daga Saudiyya Kawai Sai Ta Tarar Da Kyautar Mota Daga Wani Bawan Allah Hoto: @queenomobolanle
Asali: Instagram

Sarauniyar, a wata wallafa da ta yi, ta bayyana cewa ya zama dole ta nuna godiyarta a idon duniya saboda ba kasafai mutane ke aikata hakan ba a yanzu.

An gano ta a bidiyon tana dana motar tata. Ta kara da cewa dawowa gida da tayi ta tarar da irin wannan yautar alama ce ta Allah ya amsa addu’o’inta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta rubuta a shafin nata:

“A wannan lokaci da dabiu ke kara lalacewa sannan tashin hankali ke kara yawa, yana da kyau a dunga shafe lokaci wajen nuna godiya. Ko da harsuna miliyan godiyata ba za ta taba isa ba a nan wasu alamu ne da ke nuna Istijabah domin dawowata kenan daga kasa mai tsarki (Mecca) sai ga kyautar mota daga wani bawan Allah..Kada Allah yasa jiyanmu ya fi gobenmu wani ya ce Amin Alliamdulilahi Robili Alamin. Ina taya kaina murna.”

Kara karanta wannan

'Na shafe tsawon shekaru 16 ina daukar ciki': Uwar Yara 12 Ta Bayyana Yadda Ayi Mata Tiyata Sau 6

Likafa ta ci gaba: Matan marigayi Alaafin na Oyo sun baje kolin sabbin gidajen da suka mallaka

A wani labarin, mun kawo cewa kimannin watanni biyu bayan rasuwar Alaafin na Oyo, Lamidi Adeyemi III, matansa Gimbiya Opeyemi Omobola da Moji sun nuna sabbin katafaren gidajensu.

Matan marigayi sarkin wadanda suka cika da godiya sun jinjina masa tare da addu’an Allah ya ji kansa.

Moji ta gode ma marigayi Alaafin sannan ta tabbatar da cewar mutuwarsa ta zo kwatsam amma tarihin da ya kafa zai ci gaba da wanzuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng