Tashin hankali ga 'yan Arewa mazauna Kudu, 'yan IPOB sun kashe 'yan Nijar 8, sun gudu da kan wani

Tashin hankali ga 'yan Arewa mazauna Kudu, 'yan IPOB sun kashe 'yan Nijar 8, sun gudu da kan wani

  • Majiyoyi daga kudancin Najeriya na bayyana cewa, Hausawa na zaman dar-dar yayin da 'yan IPOB suka farmaki mazauna
  • Wannan lamari ya haifar hargitsi yayin da aka kashe mutane takwas tare da yin awon gaba da kan wani bayan yanke shi
  • Ana yawan samun kisan gilla daga 'yan IPOB a kan Hausawa mazauna yankin saboda nuna kyamar kabilar Hausawa

Owerri, jihar Imo - Tsoro ya shiga wa 'yan Arewa mazauna Owerri, babban birnin jihar Imo, biyo bayan kashe wasu 'yan Nijar takwas da 'yan kungiyar IPOB suka yi.

Harin dai ya faru ne a ranar Litinin din da ta gabata lokacin da maharan suka kai hari a wani gini da ke Orogwe, Owerri, wanda galibin Hausawa bakin haure ne daga Najeriya da Jamhuriyar Nijar ke rayuwa a ciki.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun harbi shugaban 'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa

Yadda Hausawa ke cikin tashin hankali a Imo
Tashin hankali ga 'yan Arewa mazauna Kudu, 'yan IPOB sun hallaka 'yan Nijar 8, sun gudu da kan wani | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

‘Yan Arewa a yankin sun ce an kai harin ne saboda IPOB ta dauki dukkan mutanen da ke zaune a yankin ‘yan ci-rani ne daga Arewa, ba tare da sanin wadanda abin ya shafa ba ma 'yan Najeriya bane.

Sun shaida wa Daily Trust, cewa sun shiga fargabar abin da zai faru dasu sakamakon yawaitar hare-haren da IPOB da ESN ke kai musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani ganau mai suna Abubakar Muhammad ya ce tun da farko ‘yan bindigar sun ziyarci al’ummar Hausawa a Orogwe da yammacin ranar Litinin inda suka tattauna da Hausawa mazauna yankin.

Yace:

“Lokacin da suka zo da maraice, ba sa dauke da makamai. Sun yi tattaunawar aminta da mutane; ba mu ma san 'yan bindiga ne ba.
“Amma cikin dare suka dawo suna harbin mutanenmu, nan take suka kashe mutum bakwai, mutane takwas kuma suka samu raunuka, sannan wani karin mutum daya ya mutu a asibiti, muka binne su washegari (Talata).”

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Yan Arewa Mazauna Jihar Imo Tare da Filewa Mutum Daya Kai

Muhammad wanda ke sayar da gasashen naman saniya ya yi nuni da cewa yawancin mutanen da aka kashe abokan aikinsa ne da kuma masu fataucin shanu.

An harbi 'yan Arewa matafiya

Ya kara da cewa a baya ‘yan bindigar sun harbe wasu matafiya ‘yan Arewa a ranar Lahadi.

A kalamansa, cewa ya yi:

“Sun bude wa motar bas wuta a lokacin da suka fahimci cewa matafiya ne ‘yan Arewa; da dama sun samu raunuka yayin da mutum daya kuma ya rasa ransa. Bayan kwana guda sai suka zo suka kawo mana hari a Orogwe. Yanzu dai muna rayuwa cikin dar-dar.”

Sarkin Hausawa na Jihar Imo, Alhaji Auwal Baba Suleiman, ya tabbatar wa Daily Trust cewa mutane takwas da aka kashe sun fito ne daga Jamhuriyar Nijar, kuma an sallami wasu shida da suka jikkata daga asibiti a ranar Laraba.

A kalamansa:

“An kai harin ne akasari a kan mutanen da suka mamaye wurin da suka fito daga Jamhuriyar Nijar. Suna gudanar da harkokinsu a nan; wannan (harin) yakan faru lokaci zuwa lokaci yanzu. Muna son gwamnati ta dauki wasu matakai.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da mazauna Abuja suka dage dole Buhari ya sauke ministansa da mai ba shi shawara

An yanke kan Bahaushe, an tafi dashi a Imo

Sarkin ya kara da cewa ‘yan bindigar sun yanke kan daya daga cikin wadanda aka kashe sannan suka tafi da shi.

Wani ganau ma haka ya tabbatarwa jaridar Vanguard, inda yace:

"A kan hanyarsu ne suka kashe tare da yanke kan daya daga cikin wadanda abin ya shafa da suke ganin ya kawo cikas ga abin da suke yi."

A halin da ake ciki kuma, rundunar ‘yan sandan jihar Imo a ranar Larabar da ta gabata ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai a harin da ‘yan kungiyar ta IPOB suka kai.

Kakakin ‘yan sandan, CSP Mike Abattam, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan bindigar da ake zargin 'yan IPOB ne da ESN sun zo a wata bakar mota Lexus da babura uku dauke da mutum biyu kowanne, inda suka harbe mutanen.

Ya ce ginin na wani mutum ne mai suna Sir Chima Ogbuehi, mazaunin jihar Legas.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun shiga wata jihar Arewa, sun hallaka 'yan kasuwa, sun sace matafiya 14

'Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yan Kasuwa 4, Sun Sace Matafiya 14 a Taraba

A wani labarin, akalla mutane hudu ne suka mutu a yammacin Lahadin da ta gabata, yayin da wasu ‘yan bindiga kimanin 30 a kan babura suka mamaye kasuwar Jauro Manu da ke karamar hukumar Gassol inda suka bude wuta kan wasu ‘yan kasuwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an ce sun kuma yi awon gaba da mutane shida yayin da ‘yan kasuwa suka bar hajojin su, suka gudu zuwa wani daji da ke kusa.

Wani mazaunin garin Umar Tasiu ya shaida wa jaridar cewa harin na ranar Lahadi shi ne na uku da aka kai garin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.