Zamfara: Kotun Musulunci Ta Raba Auren Shekara 23 Tsakanin Wani Mutum Da Jikarsa

Zamfara: Kotun Musulunci Ta Raba Auren Shekara 23 Tsakanin Wani Mutum Da Jikarsa

  • Wata babban kotun shari'a a karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara ta warware aure tsakanin wani mutum da jikarsa
  • Mutumin mai suna Musa Tsafe ya auri jikarsa mai suna Wasila ne tun shekaru 23 da suka gabata kuma har sun haifi yara guda takwas
  • Hukumar Hisbah, wacce ta yi kararsa a kotun ta ce tun shekarar 2020 ake ta fama da shi ya saki matar amma abin ya ci tura duk da binciken da aka yi ya nuna jikarsa ce

Zamfara - Wata babban kotun shari'a da ke Tsafe, a karamar hukumar Tsafe na Jihar Zamfara a ranar Talata ta raba auren shekaru 23 tsakanin wani mutum Musa Tsafe da jikarsa, Wasila.

Yayin yanke hukuncin, alkalin kotun, Malam Bashir Mahe, ya raba auren bayan ya saurari bangarorin biyu wato masu kare da wadanda aka yi kara.

Kara karanta wannan

Allah ya bada sa’a: Fitaccen Farfesa Yana Goyon Bayan Tsige Buhari da Gwamnoni

Taswirar Jihar Zamfara.
Zamfara: Kotun Musulunci Ta Raba Auren Shekara 23 Tsakanin Wani Mutum Da Jikansa. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Mahe ya ce auren tsakanin Tsafe da Wasila bai hallarta ba a koyarwar addinin musulunci.

Alkalin ya ce aure tsakanin mata da mijin ya saba wa sura ta 3 aya ta 23, shafi da shafi na 79 da 77 na ihkamil Ihkami.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya yi bayanin cewa an yanke hukuncin ne bayan wanda aka yi kara ya gaza kare kansa daga zargin da aka shigar kansa.

Hukumar Hisbah ne ta shigar da kara inda ta nemi a raba auren na shekaru 23.

Hisbah ta shaidawa kotu cewa auren tsakanin Tsafe da Wasila ya saba wa dokokin addinin musulunci da shari'a.

Hukumar ta ce hakan ya tilasta mata shigar da karar bayan Kwamitin Shura da masarautar Tsafe tun 2020 sun yi kokarin raba auren amma bai yiwu ba.

Binciken da kungiyoyin musulunci da dama suka yi ya nuna jikarsa ce, Hisbah

Kara karanta wannan

Buhari: Mun Ba Wa Jami'an Tsaro Cikakken 'Yanci Su Kawo Karshen Ta'addanci

Lauyan hukumar Hisbah, Malam Sani Muhammad, ya shaida wa kotu cewa binciken da kungiyoyin musulunci da dama suka yi ya nuna cewa akwai alaka ta jini tsakanin ma'auratan da suka yi aure tun 1999 don haka auren bai hallasta ba.

Muhammad ya ce auren ya saba da koyarwar addinin musulunci kamar yadda ya zo a sura ta uku aya na 23 a cikin alkur'ani mai girma.

Don haka, ya roki kotun ta raba auren.

Kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, ta rahoto cewa Tsafe ya haifi yara takwas tare da Wasila.

Kaduna: Ana Rikici Kan Katifa Tsakanin Miji Da Mata Da Ke Son Kashe Aurensu A Kotun Shari'a

A wani rahoton, wata kotun shari'a a Kaduna, a ranar Litinin ta umurci wata mata mai neman saki, Halima Ahmad ta mayar da katifa ga mijinta da suka kwance alaka, Suleiman Atiku.

Mr Atiku, ma'aikacin hukumar gyaran hali, tunda farko ya bukaci a dawo masa da katifansa, kafin ya amince da bukatar sakinta, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ke duniya: A kan N50,000, matashi ya halaka kawar kanwarsa, ya birne gawarta a dakinsa

Halima, wacce ke zaune a Badarawa, Kaduna, a watan Afrilun 2022, ta garzaya kotun shari'a da ke zamanta a Magajin Gari, Jihar Kaduna ta nemi a raba ta da mijinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164