Buhari: Mun Ba Wa Jami'an Tsaro Cikakken 'Yanci Su Kawo Karshen Ta'addanci
- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta bai wa jami;an tsaro cikakken yanci domin su kawo karshen yan ta'adda a kasar
- Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya ke mika sakon ta'aziyya ga fatan samun lafiya ga wadanda yan ta'adda suka kaiwa hari a Sokoto, Kaduna da Plateau a baya-bayan nan
- Shugaban na Najeriya ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin cigaba da bawa jihohi tallafa a kokarin da ake na samar da zaman lafiya mai dorewa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta bawa hukumomin tsaro 'cikakken dama' domin kawo karshen hare-hare a kasar.
A cikin sanarwar da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa ya fitar, Buhari ya bayyana hare-haren da aka yi a Sokoto, Plateau da Kaduna a matsayin 'tsageranci'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari, wanda ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya faru da su, ya tabbattarwa gwamnatin jihohi cewa gwamnatinsa za ta cigaba da yin duk abin da ya dace don inganta tsaro.
"Mun bawa jami'an tsaro cikakken dama domin su kawo karshen wannan hauka," kamar yadda aka ambato ya ce.
"Na yi Allah wadai da wannan hare-haren a kasar. Ina tabbatarwa jihohi cewa za mu cigaba da bada duk tallafi da ta dace daga gwamnatin tarayya.
"Ina mika addu'a da ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa. Ina yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa," in ji Buhari.
A ranar 1 ga watan Agusta, an rahoto yan bindiga sun sace a kalla mutum 50 daga garin Damari a karamar hukumar Birnin Gwari na Jihar Kaduna.
A dai ranar, an kashe mutum bakwai, yayom da wasu biyu - ciki da yaro - sun jikkata, bayan harin da aka kai a kauyen Danda Chugwi a karamar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Plateau.
Bayan hare-hare a Sokoto, Kaduna da Plateau, an rika kaiwa mutane hare-hare, hukumomin tsaro da gine-ginen gwamnati a sassan kasar.
Asali: Legit.ng