An Dauke Wuta Ana Tsaka Da Aikin Tiyata, Mara Lafiya Ta Mutu

An Dauke Wuta Ana Tsaka Da Aikin Tiyata, Mara Lafiya Ta Mutu

  • Wani Magidanci ya Zargi cibiyar kula da cututtuka da kuma tiyata ta jihar Ondo da sakaci bayan matarsa ta rasu yayin da ake yi mata tiyata
  • Sunday Samuel ya ce matar sa mai ‘ya’ya hudu ta dade tana fama da cutar kansar nono kafin ta rasu
  • Matar Sunday Fola ta rasu a asibiti a lokacin da likitoci suke mata aikin tiyata yayin da ma’aikatar lafiya ta rika musayar wuta da janareta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Ondo - Wani magidanci mai suna Sunday Samuel, ya zargi cibiyar kula da cututtuka da kuma tiyata ta jihar Ondo da ke cikin birnin Ondo da sakaci bayan matarsa ta rasu yayin da ake yi mata tiyata a cibiyar.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayiyar Fola tana fama da cutar kansar nono.

Bayan haka an sanya wa matar mai ‘ya’ya hudu magani na kusan wata guda a asibiti domin shiryata ga aikin tiyata a ranar Litinin, 25 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Jarumar Mata: Yadda Uwargida Ta Rungume Amaryar Mijinta A Wajen Dinan Aurensu, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

surgical
An Dauke Wuta Ana Tsaka Da Aikin Tiyata, Mara Lafiya Ta Mutu FOTO PUNCH
Asali: UGC

A cewar mijin nata, aikin ya samu cikas ne sakamakon katsewar wutar lantarki, yayin da ma’aikatar lafiya ta rika musayar wuta da janareta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma koka da yadda asibitin ya kasa samar da injin iskar oxygen na jiran aiki kafin a fara aikin tiyatar, saboda babu ko daya a lokacin da suke bukata yayin aikin.

Samuel ya ce duk hakan yana ta faruwa ne yayin da ake ci gaba da yiwa matar sa aikin tiyata. Bayan kusan awa daya, wanda ke kula da janareta ya sake komawa wutar lantarki ta NEPA.

Bayan kusan awa daya da mintuna 30, shine daya daga cikin likitocin ya fito ya kira wani a gaban mu domin ya samo iskar oxygen da za a sa mata.

Samuel ya ce :

Daga baya ne suka fito suka ce min matata ta mutu. A lokacin ne na fashe da kuka.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

Samuel ya kara da cewa ya biya duk bukatun asibitin kafin a kai Fola cibiyar kula da lafiya dan gudanar da aikin tiyata.

An Riga An Zabi Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A APC, Inji El-Rufai

A wani labari kuma, Gabanin zaben 2023, an zabi babban darakta a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC). Rahoton Channels TV

Wannan shine jawabin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya bayyanawa manema labarai a ranar Litinin bayan ganawar da gwamnonin APC suka yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, da abokin takararsa Kashim Shettima, a Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa