Baba-Ahmed Ya Bayyana Matsayar Peter Obi A Kan Kungiyar IPOB Ta Nnamdi Kanu

Baba-Ahmed Ya Bayyana Matsayar Peter Obi A Kan Kungiyar IPOB Ta Nnamdi Kanu

  • Datti Baba-Ahmed, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben shekarar 2023 ya ce Peter Obi, abokin takarsa baya goyon bayan haramtaciyyar kungiyar IPOB
  • Baba-Ahmed, cikin hirar da aka yi da shi ya ce sai da ya yi bincike ya tabbatar Obi ba shi da alaka da IPOB kafin ya amince ya zama abokin takararsa
  • Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya kuma karyata cewa a lokacin Peter Obi na gwamnan Anambra an rika yi wa yan arewa rashin adalci yana mai cewa tun farfaganda ce ta siyasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Datti Baba-Ahmed, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsu, Peter Obi, baya goyon bayan kungiyar IPOB da ayyukan da ta ke yi, rahoton Daily Trust.

Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a lokacin da aka yi hira da shi a shirin Daily Politics na Trust TV a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Ba Zamu yi APC a zabe 2023 ba: Kiristocin Jihohin Arewa 19 Sun Jaddada

Baba-Ahmed
Baba-Ahmed Ya Bayyana Matsayar Peter Obi A Kan Kungiyar IPOB. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

"Ban yarda cewa Peter Obi yana goyon bayan kungiyar IPOB ba domin idan hakan gaskiya ne da yanzu bana tare da shi," in ji shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa babu hujjan da ke nuna wannan zargin gaskiya ne.

Ya ce:

"Irin wannan hirar aka yi a kai na a lokacin da na ce ina son a rika kira na dan Najeriya don zaben shekarar 2023. Babu abin da mutane ba za su iya fada ba. Ko yau da safe, sai da na kira taron manema labarai saboda yawan labaran karya da ke yawo ... har yanzu babu hujjan da ke nuna gaskiya a zargin."

Baba Ahmed ya kara da cewa kafin ya amince ya zama abokin takarar Obi, sai da ya yi bincike a kansa ya tabbatar babu abin da ya hada tsohon gwamnan na Anambra da IPOB.

Kara karanta wannan

2023: Babachir Lawal Ya Bayyana Yadda Kiristocin Arewa Za Su Yaki Tikitin Musulmi Da Musulmi

"Misali, sun ce ba a yi wa yan arewa adalci ta hanyar umurtarsu su rika yawo da katin shaidan zama a jihar, kafin in amsa zan yi takara tare da Obi. Cikin yan makonni, na yi dukkan binciken da zan iya. Akwai wayoyi masu kyamara, na tambaya har na ce zan bada tukwici idan an nuna min wanda ya ce lokacin da Peter ke gwamna an tilast min saka wannan. ba a samu kowa ba.
"Kana son in zauna in rika sauraron mutanen da ke magana barkatai saboda ka fito siyasa idan na san irin siyasar da muke yi."

2023: Babban Sanatan APC Ya Bayyana Abubuwa 2 Da Za Su Hana Tsige Buhari

A wani rahoton, jigo a jam'iyyar APC, Sanata Adeseye Ogunlewe, ya ce dalilai na addini da kabilanci ne za su kawo cikas ga yunkurin da wasu yan majalisar tarayya ke yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Atiku: A kwana 100 zan fara gyara tattalin arziki, in yaki rashin tsaro idan na gaji Buhari

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a Arise TV a ranar Alhamis 28 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel