Jerin Yawan Mutanen Da Suka Yi Sabuwar Rijistar Zaɓe Na Kowane Yanki, Arewa Ta Yi Zarra
- Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta tattara sabbin Rijistar katin zaɓe miliyan 12m cikin watanni 13 da suka shuɗe
- Bayan kammala aikin sabuwar rijistar a watan Yuli, Alƙaluman da aka tattara sun nuna yawan mutane da suka yi a kowane shiyya
- Shiyyar Arewa maso yamma da ke fama da matsalar yan bindiga ita ce kan gaba a yawan mutanen da suka fito suka yi rijistar zaɓe
Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta samu sabbin mutanen da suka yi rijistar katin zaɓe miliyan 12m a cikin watanni 13 yayin da wa'adin da ta ware don yin rijistar ya ƙare.
INEC ta sanya wa'adin ranar 31 ga watan Yuli, 2022 a matsayin ranar da zata rufe yin Rijistar zaɓe wanda kuma ya ƙare kwana biyu nan baya.
A wasu Alƙaluma da The Cable ta fitar a shafinta, ya nuna cewa a cikin shiyyoyi Shida da muke da su a Najeriya, shiyyar arewa maso yamma ce kan gaba a yawan rijista.
Kudu maso kudancin Najeriya ke mara wa shiyyar baya sai kuma shiyyar arewa ta tsakiya yayin da shiyyar Kudu maso gabashin Najeriya ya zamo na ƙarshe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jerin yawan sabbin rijista na kowane shiyya
Arewa maso yamma: 2,514, 273
Kudu Maso Kudanci: 2, 458, 095
Arewa ta Tsakiya. 2,314, 358
Kudu Maso Yammaci: 2,039, 982
Arewa Maso Gabas: 1, 531,070
Kudu Maso Gabashi: 1, 441,156
A wani labarin kuma Kwamishinan Gwamnan Arewa Ya Bi Sahun Wasu Jiga-Jigan PDP, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC
Ɗaya daga cikin kwamishinonin da gwamna Aminu Tambuwal ya maida kan kujerun su ya sauya sheƙa daga APC zuwa PDP.
Kanal Garba Moyi mai ritaya ya bi sahun shugaban ƙaramar hukuma da wasu Kansiloli da suka koma APC jiya.
Asali: Legit.ng