Bayan Barazanar Gwamna El-Rufai, Malaman Jami’a Sun Koma Aiki a Kaduna

Bayan Barazanar Gwamna El-Rufai, Malaman Jami’a Sun Koma Aiki a Kaduna

  • Daliban da ke karatu a jami’ar KASU sun soma rubuta jarrabawar karshe a shekarar 2021/22
  • A ranar Litinin aka ji cewa daliban wannan jami’a da ke Kaduna suna aji, wajen zana jarrabawa
  • Wannan mataki ya zo ne bayan jin Nasir El-Rufai yana barazanar korar malaman da ke yajin-aiki

Kaduna - Duk da yajin-aikin da kungiyar ASUU ta ke yi a Najeriya, sai aka ji labari cewa daliban jami’ar jihar Kaduna watau KASU sun fara yin jarrabawa.

Rahoton da ya fito daga Leadership ya bayyana cewa daliban jami’ar ta KASU sun soma rubuta jarrabawar shekarar karatu na 2021/2022 a ranar Litinin.

Bayan watanni biyar da rufe jami’o’i, ana rubuta jarrabawar zango na biyu na shekarar 2021/22. Daliban sauran makarantu na cigaba da zaman gida.

Kara karanta wannan

Rarara Ya Shirya Taron Saukar Al-qurani Don Samun Zaman Lafiya A Kasar, Jarumai Maza Da Mata Sun Hallara

Za a kori masu yajin-aiki a Kaduna

Jami’ar ta dauki wannan mataki ne jim kadan bayan an ji gwamna Nasir El-Rufai yana barazanar sallamar duk wani malamin da ya cigaba da yajin-aiki.

Mai girma El-Rufai ya bukaci malaman KASU su koma bakin-aiki tun da a cewarsa, ASUU tana rigima da gwamnatin tarayya ne ba da jihar ta Kaduna ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar tace ta zagaya cikin jami’ar a ranar Litinin, kuma ta ga dalibai a dakunan karatu sun dukufa suma rubuta jarrabawa, ga ma’aikata suna duba su.

Gwamna El-Rufai
Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

Tun makon jiya ya kamata a koma aiki

Wani dalibi mai suna Sani Abdullahi ya shaidawa manema labarai cewa tun a makon jiya ya kamata a fara jarrabawar, amma aka dakata sai zuwa jiya.

A cewar Abdullahi, hutun kwanaki uku da Gwamnatin jihar Kaduna ta bada domin a mallaki katin zabe ya jawo aka gaza fara jarrabawar a makon da ya wuce.

Kara karanta wannan

Daliban Najeriya sun shiga tasku: ASUU ta tsawaita yajin aikinta zuwa karin wasu makwanni masu yawa

Dalibin yake cewa dogon yajin-aikin da kungiyar ASUU ta tafi ya yi tasiri a kan malamansu domin ba su shiga aji sosai a duk tsawon wannan lokacin ba.

‘Yan jaridar sun nemi jin ta bakin ‘yan kungiyar ASUU na reshen jami’ar jihar ta KASU, amma abin ya gagara, domin malaman ba su yarda sun ce komai ba.

Baya ga jami’ar KASU akwai tsirarrun jami’o’in da malamansu ba su shiga yajin-aiki ba, amma an rufe kusan duka jami'o'in gwamnatocin tarayya da na jihohi.

Barazanar Nasir Ahmad El-Rufai

A baya rahoto ya zo cewa Nasir Ahmad El-Rufai ya ja-kunnen malaman da ke yajin-aiki.

"Idan Malaman Jami'ar Jihar Kaduna KASU suka cigaba da yajin aiki Wallahi Tallahi Billahi, zamu iya tashi rana daya dukkan su muce mun kore su, kuma mu buga a jarida mu dauki wasu aiki.
Matsalar ASUU bada jihar Kaduna bane da Gwamnatin tarayya ne; ita kuma KASU ta Gwamnatin Jihar Kaduna ce."

Kara karanta wannan

Yadda Malamar Jami’a Ta Koma Tallan Dankali Saboda Yajin Aikin ASUU

- Mallam Nasir El-Rufai

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng