Ba Zai Yiwu Ba: Pantami Ya Tubure, Ya Ce Ba Zai Bari a Kara Harajin Katin Waya da Data Ba

Ba Zai Yiwu Ba: Pantami Ya Tubure, Ya Ce Ba Zai Bari a Kara Harajin Katin Waya da Data Ba

  • Ministan sadarwa da tattalin arzikin Najeriya ya tubure, ya ce sam ba zai bari a kara wa 'yan Najeriya kudin harajin katin waya da data ba
  • Pantami ya ce fannin tattalin arzikin sadarwa ya taka rawar gani wajen ganin tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa matuka
  • Hakazalila, Pantami ya bukaci gwamnati ta duba wasu fannonin tattalin arziki domin kara haraji ba a ma'aikatarsa ba

Jihar Legas - Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital Isa Pantami ya yi fatali da sabon yunkurin da gwamnatin tarayya ta yi na kara harajin kashi biyar cikin 100 a harkokin sadarwa.

Idan aka aiwatar da hakan, zai zama 'yan Najeriya za su fara biyan 12.5% cikin 100% a matsayin haraji daga katin waya ko data da suka saya domin amfaninsu, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

An samu ci gaba: Minista Pantami ya haramta shigo da layukan waya daga kasashen waje

Pantami ya ce ba za a kara kudin Data da katin waya ba
Ba zai yiwa ba: Pantami ya tubure, ya ce ba zai bari a kara kudin katin waya da Data ba | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a Legas a wani bikin baje kolin da ofishin bunkasa sashen sadarwa na Najeriya, wanda hukumar sadarwa ta Najeriya ta shirya.

A cewarsa, fannin sadarwa ya riga ya ba da gudummawa sosai ga tattalin arzikin Najeriya, kuma karin harajin na iya yin illa ga ci gabanta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bukaci gwamnati da ta yi la’akari da sanya haraji ga sauran sassa na tattalin arzikin da ba su taimaka wa ci gaban kasar ba, haka nan jaridar BluePrint ta tattaro.

Ci gaba: Minista Pantami ya haramta shigo da layukan waya daga kasashen waje

A wani labarin, a ranar Litinin ne muke samun labarin cewa, gwamnatin tarayya ta sanar da hana shigo da layukan waya da aka fi sani da SIM a kasar.

Kara karanta wannan

Daliban Najeriya sun shiga tasku: ASUU ta tsawaita yajin aikinta zuwa karin wasu makwanni masu yawa

Ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital na kasar Farfesa Isa Pantami ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a birnin Legas.

Jaridar PM News ta ce, Panta ya bayyana haka ne a wajen bikin baje kolin kamfanonin sadarwa na kasa (NTICE) wanda ofishin bunkasa fasahar sadarwa ta Najeriya (NODITS) na Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ya shirya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.