Yan Luwadi Shida Sun Shiga Hannu A Nasarawa, Yan Sanda Sun Gargadi Mazauna Jihar

Yan Luwadi Shida Sun Shiga Hannu A Nasarawa, Yan Sanda Sun Gargadi Mazauna Jihar

  • Jami'an yan sanda a jihar Nasarawa sun shiga hannu da wasu masu laifi har su shida
  • Wasu yan damfara da ke amfani da manhajar kulla soyayya tsakanin yan luwadi sun shiga hannu
  • Wadanda ake zargin suna yaudarar mutane a matsayin yan luwadi sannan su raba mutum da dukiyarsa idan ya fada tarkonsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Nasarawa - Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta kama wasu migayu su shida wadanda suke damfarar jama’a ta manhajar kulla alaka tsakanin yan luwadi.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Lafia a ranar Lahadi, ya ce yadda masu laifin ke aikinsu shine shirya haduwa da wadanda suka fada komadarsu.

Yan sanda
Yan Luwadi Shida Sun Shiga Hannu A Nasarawa, Yan Sanda Sun Gargadi Mazauna Jihar Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya kuma ce da zaran sun yi nasarar yaudarar mutanen zuwa inda suke, sai su kwace masu kayayyakinsu ta karfin tuwo, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yadda Matasa 3 Suka Kama Sana’ar Kosai, Sun Mayar Da Hankali Wajen Ganin Sun Yi Kudi, Hotunansu Ya Yadu

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A ranar 31 ga watan Yuli, 2022, da misalin karfe 07:20 na safe, yayin da ake gudanar da aiki bisa ga bayanai abun dogaro, Jami’an yan sanda da ke aiki a sashin Masaka, karamar hukumar Karu sun farmaki mabuyar wasu guggun miyagu, inda suka kama mutane kamar haka: Sunday Michael, Luka Musa, Joy Sunday, Elijah Ishaya, Agafa Sandra da Abdulrahman Tijani.
“Binciken farko ya nuna cewa masu laifin sun hada kai a tsakaninsu sannan suna amfani da wani shahararren manhajar kulla soyayya ta yan luwadi suna haduwa da mutane daga yankuna daban-daban na kasar, suna kawosu mafakarsu sannan su kwace masu kayayyakinsu.
“An kwato kudi N150,000 da suka karba daga wani da ya fito daga jihar Imo a ranar 30 ga watan Yulin 2022.
“Wadanda ake zargin sun tona cewa zuwa yanzu sun yaudari mutum takwas ta wannan hanya kuma sun samu kudi N1,360,000 daga hannun mutanen a lokuta mabanbanta.”

Kara karanta wannan

Harin Kwanton Bauna: Yan Bindiga Sun Afka Wa Tawagar Yan Sanda Sun Kashe Jami'i Daya

Nansel ya ce kwamishinan yan sandan jihar, Adesina Soyemi, ya bukaci jama’a da su kula da irin abokan da suke hulda da su a soshiyal midiya.

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 6 A Katsina, Sun Nemi A Biya Kudin Fansa Miliyan N50

A wani labarin, tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da mutane shida a Tashan Buja da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Maharan sun farmaki kauyen ne da misalin karfe 12:30 na tsakar daren Juma’a ba tare da harbi ba sannan suka dauke wata matar aure, danta da wasu mutane shida, jaridar Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng