Labari Da Duminsa: DSS Ta Kama Shugaban Boko Haram a Ogun
- Jami'an hukumar yan sandan farin kaya ta Najeriya wato DSS sun yi nasarar kama wani da ake zargin shugaban yan Boko Haram ne a Ogun
- Majiya kwakwara daga hukumomin tsaro ta tabbatar da kama wanda ake zargin, tana mai cewa sai da aka yi gumurzu sannan aka ci galaba a kansa
- Majiyar ta kara da cewa a daren ranar Lahadi aka kama shi kuma yana hannun DSS amma kakakin DSS Peter Afunanya bai ce komai ba game da lamarin
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Ogun, Abeokuta - Ana zaman dar-dar a Abeokuta, Jihar Ogun, a ranar Lahadi, bayan kama wani da ake zargin shugaban kungiyar Boko Haram ne.
Hukumar yan sandan farin kaya, DSS, ce ta kama wanda ake zargin kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wata majiya kwakwara ta shaida wa Daily Trust cewa an kama wanda ake zargi shugaban ne a Boko Haram din a unguwar Ijaye a Abeokuta.
Majiyar ta ce da farko wanda ake zargin ya nuna tirjiyya amma daga bisani DSS ta yi galaba a kansa.
An kama shi ne a cikin dare, majiyar ta shaida wa Daily Trust a daren ranar Lahadi.
Majiya daga hukumar tsaro ta ce ya tafi Abeokuta ne domin kafa sansani na garkuwa da mutane da kai hare-hare.
Amma, bayan tattara bayanan sirri, jami'an DSS da bindiga suka afka mabuyarsa suka kama shi.
"Ba abu mai sauki bane. Bayannan sirri da ikon Allah ya taimaki jami'an. Akwai irin su da yawa, amma ba barci muke ba" in ji majiyar.
Wakilin majiyar Legit.ng ya ce har yanzu wanda ake zargin yana hannun DSS.
Hakan na zuwa ne a lokacin da ake zargin yan ta'adda na shirin kai hari a wasu jihohin kudu maso yamma.
Martanin hukumomin tsaro kan kamen
Da aka tuntube shi, Kakakin DSS, Dr Peter Afunanya, bai tabbatar ba kuma bai musanta kamen ba.
"Ba zan ce komai ba" ya ce a yayin da ya ke amsa sakon tes da aka tura masa.
Kakakin yan sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce ba shi da labarin kamen.
Asali: Legit.ng