Yadda Matasa 3 Suka Kama Sana’ar Kosai, Sun Mayar Da Hankali Wajen Ganin Sun Yi Kudi, Hotunansu Ya Yadu
- Wani matashi dan Najeriya, Alarma Abd-Karim Isola, ya baje kolin wasu hazikan matasa uku da ke siyar da kosai a bakin hanya
- Isola ya bayyana cewa yayin da mutane ke tsoron ko matasan na da hatsari, shi ya kan siya kosai a wajensu don sauya wannan tunani
- Mutane da dama sun yi martani a kan hotunan matasan wadanda suka yi matukar birge su, sun ce su abun koyi ne a cikin al’umma
Wani dan Najeriya mai suna Alarma Abd-Karim Isola a Facebook a ranar Laraba, 27 ga watan Yuli, ya je shafinsa don rubuta labarin wasu hazikan matasa uku a Offa.
Ya ce matasan sun bude sana’ar siyar da kosai sannan suka mayar da hankali a kai. A cewarsa, shekarunsu na a tsakanin 20-25.
Bidiyon Yadda Gwamna Zulum Ya Zage Da Kansa Ya Daidaita Cunkoson Jama’a A Wajen Daurin Auren Yar Shettima
Mutane sun zata yan Yahoo ne
Isola ya bayyana cewa matasan wadanda ba yan gari bane sukan kasance cikin kyakkyawan shiga kuma suna faran-faran yayin hulda da abokan cinikinsu. Ya kara da cewa suna dauke da askin da ake yiwa lakani da na ‘Yan Yahoo’.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sanyawa wajen suyar kosansu “akara yahoo” saboda daukar da mutane ke yi masu da farko; cewa suna amfani da sana’ar ne don yin rufa-rufa a kan damfara da asiri.
Kosansu akwai dadi
Don tallafawa kasuwancinsu, Isola ya ce:
“Ina yawan siyan kosai a wajensu don karfafawa mutane gwiwar cewa babu matsala kuma ba sa kwashe arzikin mutane (ban ga laifin kowa ba a kan irin wannan tsoron).”
Ya bayyana cewa kosansu akwai dadi kuma suna yinsa ne cike da tsafta.
Ya kara da cewa:
“A duk sand aka shiga Offa, ka tsaya a gefen Captain Cook sannan ka dandana akara yahoo.”
Allah ya albarkace su
Debo Adedayo ya ce:
“Wannan abun sha’awa ne! Allah Ubangiji ya albarkaci nemansu.”
Akeem Afolabi ya ce:
“Suna nan a Ibadan, Osogbo da sauransu. Allah ya albarkaci nemansu.”
Abdulkareem Hassan Olayinka ya ce:
“Ina addu’a Allah yasa wannan kasuwanci ya kai su inda suke mafarkin zuwa.”
Sulaimon Blacky ya ce:
“Ku ci gaba da aikin nagari.”
Kin Gama Mun Komai a Rayuwa, Lauya Ya Fashe Da Kuka A Gaban Mahaifiyarsa Kan Dawainiyar Da Ta Yi Da Shi
Agefe guda, wani bidiyo mai taba zuciya da ya yadu a shafukan soshiyal midiya ya nuno wani lauya da aka rantsar a matsayin cikakken lauya yana godiya ga mahaifiyarsa cike da kauna.
A cikin dan gajeren bidiyon, an gano matashin mai suna Harmonihie zube a gaban mahaifiyarsa yana zubar da hawayen murna da godiya.
Matashin ya rike kafafuwan mahaifiyar tasa yayin da yake kuka wiwi, yana godiya gare ta a kan goyon bayan da ta bashi a wannan tafiya na zama lauya.
Asali: Legit.ng