Harin Kwanton Bauna: Yan Bindiga Sun Afka Wa Tawagar Yan Sanda Sun Kashe Jami'i Daya

Harin Kwanton Bauna: Yan Bindiga Sun Afka Wa Tawagar Yan Sanda Sun Kashe Jami'i Daya

  • Wasu yan bindiga da ake zargin yan kungiyar asiri ne sun kai wa tawagar yan sanda harin kwanton Bauna sun kashe jami'i guda daya a Bayelsa
  • Mai magana da yawun yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da harin yana mai cewa dan sandan da aka harba ya mutu ne bayan an kai shi asibiti
  • SP Butswat ya kuma ce yan sandan sun yi nasarar fatattakar yan bindigan har suka kora su cikin daji tare da raunata wasu daga cikinsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bayelsa - Wasu yan bindiga da ake zargin yan kungiyan asiri ne, a safiyar ranar Asabar sun kai wa motar sintiri na yan sanda harin kwanton bauna a Banga Camp kan gadar Swali a karamar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa, inda suka kashe jami'i daya.

Kara karanta wannan

An Kori Dan Sandan Da Aka Nadi Bidiyonsa Yana 'Halasta' Wa Kansa Karbar Cin Hanci

Wata majiya daga garin Swali ta shaida wa Daily Trust cewa bata garin sun mamayi jami'an tsaron ne suka yi musayar wuta na tsawon wani lokaci.

Taswirar Bayelsa.
Yan Bindiga Sun Afka Wa Tawagar Yan Sanda Sun Kashe Jami'i Daya. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar majiyar, maharan sun kuma harba wasu ababen fashewa, wanda ya janyo hayaki da dama suka cika yankin.

An kuma gano cewa yan sandan da ke aiki sun yi nasarar dakile harin suka fattaki maharan zuwa wani daji da ke kusa da wurin.

Martanin rundunar yan sanda

Kakakin yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce jami'an rundunar na bin sahun maharan, yayin da ake cigaba da bincike kan afkuwar harin.

Ya tabbatar da cewa yan bindigan sun harbi dan sanda daya kuma daga baya ya mutu a asibiti.

Ya ce maharan sun tsere cikin daji tare da raunukan bindiga, yayin da wani dan sanda da yaro da aka harba suna asibiti ana musu magani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164