Matata Sai Ta Karbi Kudi A Hannu Na Kafin Ta Yarda Muyi Kwanciyar Aure, Yarima Ya Fada Wa Kotu
- Wani mutum, Adegbenga Dada, wanda yarima ne daga jihar Kogi ya yi ƙarar matarsa a kotu yana neman a raba auren
- Dada, ya shaidawa kotu cewa yana son a raba aurensa da matarsa saboda sai ya biya ta kudi suke kwanciyar aure kuma tana bin wasu mazajen a waje
- Roseline, wacce Adegbenga ya yi kara a kotun ita ma ta yarda a raba auren su amma ta nemi kotun ta mallaka mata wani gida da Adegbenga ya gina a Legas
Mr Adegbenga Dada, Injiniya wanda kuma yarima ne daga Eruku a karamar hukumar Ekiti na Jihar Kogi, ya ce matarsa na neman ya biya kudi kafin ta yarda su yi kwanciyar aure, rahoton Daily Trust.
Ya bayyana hakan ne cikin ƙarar da ya shigar a babban kotun da ke zamanta a Ilorin. Dada na neman a raba auren su na shekara 28 kan zargin Roseline Dada da alaka da wasu mazaje a waje.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya yi zargin bin mazaje da Dada ke yi na shafan ayyukan ta na gida, ya kara da cewa tana aikan yaran ta mata wurin abokanta maza su karbo mata kuɗi.
A cewar Adegbenga, wanda dan asalin jihar Kwara ne, amma mazaunin Legas, "Matata ta dena kwana a dakin mu ta koma dakin baki. Ta kan dage cewa idan ba biya wani adadin kuɗi da ta nema ba, ba za ta yi kwanciyar aure da ni ba. Idan har ban biya kudin ba, ba za ta yarda ba.
"Auren ya lalace domin ni da matata ba mu iya zama mu tattauna kan rayuwar mu da na yayan mu."
Ya kuma roki kotun ta bashi daman rike yaransu uku.
Martanin Roseline
Matar, Roseline a martanin ta ta musanta zargin cewa tana bin mazaje.
Amma, ta ce tana goyon bayan raba auren sai dai ta nemi kotu ta mallaka mata gidansu na Legas wanda ta ce tare suka gina da wanda ya yi ƙarar nata.
Yayin shari'ar, wanda ya yi ƙarar, ta bakin lauyansa, Me Josiah Adebayo, ya ce hotunan matar ba tufafi tare da masoyinta da aka ciro daga wayanta kawai hujja ne ba don kunyata ta ba.
Hukuncin kotu
Yayin yanke hukunci, Mai shari'a S.T. Abdulaqadri, ta amince da raba auren tana mai cewa hujjojin da aka gabatarwa kotu kan wanda ake kara sun gamsar da ita.
Ta kuma ce wanda aka yi ƙarar ta, Mrs Dada bata da wani kaso a gidan wanda ya shigar da karar a Legas.
Amma bata mallaka wa kowa cikinsu hakkin rikon yaran su uku ba, tana mai cewa yaran sun haura shekaru 20 don haka ba ƙananan yara bane.
Asali: Legit.ng