Hadimin Gwamna Sanwo-Olu Na Jihar Legas Ya Rasu A Hadarin Mota
- Mai taimaka wa gwamna Babajide Sanwo-Olu kan harkokin ilimi, matasa da dalibai, Mista Sanyanolu ya rasu yau Jumu'a
- Babban hadimin gwamnan ya rasa rayuwarsa ne yayin da Motarsa ta bugi wani ATM a yankin Maryland yana tsaka da zabga gudu
- Tuni aka zaro gawarsa kana hukumar kai ɗaukin gaggawa ta jihar Legas ta taimaka wajen ciro motar da haɗarin ya rutsa da ita
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lagos - Babban mai taimaka wa gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas kan ilimin manyan makarantu, matasa da harkokin ɗalibai, Omotayo Sanyaolu, ya rasu.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Sanyaolu, ya rasa rayuwarsa ne a wani haɗari da Motarsa kaɗai ta yi da safiyar Jumu'a a kusa da sansanin Sojoji da ke Maryland, Ikeja, babban birnin Legas.
Yadda lamarin ya faru
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren dindindin na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas, Dakta Femi Oke-Osanyantolu, ya ce Motar mamacin ta yi karo da wani ATM da ke yankin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce:
"Lokacin da jami'ai suka isa wurin sun tarad da wata Bakar Toyota Camry mai lambar rijista LAGH 32, yayin da take tsaka da zuba gudu kan titi ta bugi abun cire kudi ATM na bankin Keystone kusa da sansanin soji, Ikeja."
"Abun baƙin cikin shi ne matashin da ke cikin motar shi kaɗai, Omotayo Sanyaolu, ya rasu nan take kuma tuni aka ciro gawarsa lokacin da masu kai ɗauki suka isa."
Ya ƙara da cewa an miƙa gawar mamacin ga jami''in sojin da ke kan aiki a lokacin mai suna Musa.
Haka nan hukumar LASEMA ta taimaka da Motarta har aka yi nasarar ciro motar da Marigayin ya yi haɗari da ita.
A wani labarin kuma Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kashe Kwamandan Yan Bijilanti a Jihar Yobe
Karin Bayani: Yan 'Boko Haram' Sun Kai Hari Hedkwatar Ƴan Sanda A Kano, Rundunar Yan Sanda Ta Yi Martani
Yan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun shiga har cikin gida, sun kashe kwamandan jami'an tsaron Sa'kai a jihar Yobe.
Bayanai sunyi nuni cewa yan ta'adda sun shiga garin Buni Yadi kuma suka nufi gidan kwamandan kai tsaye suka kashe shi.
Asali: Legit.ng