Labari da duminsa: 'Yan daba sun farmaki cocin Legas, sun sace na'urorin buga katin zabe

Labari da duminsa: 'Yan daba sun farmaki cocin Legas, sun sace na'urorin buga katin zabe

Wasu ’yan daba sun kai farmaki cocin St. Bridget Catholic da ke ljesha, Surulere Legas, tare da kwashe injinan jami’an INEC da ke aikin rajistar PVC.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Limamin cocin ya kulle harabar cocin, a lokacin da mutane suka yi tururuwa domin gudun tsira, Vanguard ta ruwaito.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa ‘yan daban sun mamaye wurin, inda suka ce ba za a bar su su yi rajistar PVC din ba saboda ba za su zabi dan takarar su ba.

Ya ce sun lalata kayayyakin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) tare da kwashe wasu kayayyakin rajistar PVC.

Ya kara da cewa an tattara ‘yan sanda zuwa yankin domin dakile taka doka da oda.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng