Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kashe Kwamandan Yan Bijilanti a Jihar Yobe
- Yan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun shiga har cikin gida, sun kashe kwamandan jami'an tsaron Sa'kai a jihar Yobe
- Bayanai sunyi nuni cewa yan ta'adda sun shiga garin Buni Yadi kuma suka nufi gidan kwamandan kai tsaye suka kashe shi
- Magajin Garin Shuwarin ya roki mutane su kai rahoton duk wani motsi da suke zargi ga jami'an tsaro
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Yobe - Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kashe kwamandan yan Bijilanti da aka fi sani da yan Sa'kai, Umaru Balami, a garin Buni Yadi, ƙaramar hukumar Gujba a jihar Yobe, arewa maso gabashin Najeriya.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa yan ta'addan sun kashe Balami ne a cikin gidansa ranar Talata.
Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya ce yan ta'addan sun shiga gari ne a kan Babura kuma suka tafi kai tsaye zuwa gidan Kwamandan jami'an tsaron, wanda a lokacin aka ce yana kwance yana bacci.
Bayanai sun nuna cewa wadan da ke tsaron kwamandan sun yi yinkurin gwabza wa da maharan amma suka ci ƙarfin su saboda sun fi su muggan makamai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Magajin Garin Shuwarin, Lawam Gujja Abubakar, ya ce:
"Mun wayi gari da mummunan labari ranar Laraba da safe kasancewar mayaƙan Boko Haram sun kashe kwamandan yan Bijilanti, Umaru Balami, a gidansa."
Ya bayyana cewa an ɗakko gawar marigayi Kwamandan jami'an daga cikin gidansa cikin jini washe garin ranar da yan ta'addan suka kai masa hari.
Magajin Garin ya yi Addu'ar Allah ya kyautata makwancin marigayin, sannan ya yi kira ga mutanen garin da baki ɗaya yankin ƙaramar hukumar Gujba da su kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ga hukumomin tsaro.
Halin da mazauna yankin ke ciki
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Litinin, mazauna yankin sun ga ayarin mayaƙan Boko Haram da motoci biyu da Mashina sun nufi yankin daga wajen gari da nufin ta da hankali.
Wata majiya mai ƙari ta tabbatar da cewa hukumomin soji sun haɗa tawaga kuma sun tura dakarun soji tare da Yan Sa'akai yankin don samar da tsaro, haka nan a Gujba.
A wani labarin kuma NSA Babagana Monguno ya ce tabarɓarewar tsaro ta mai yan Najeriya bango, sun fara fafutukar neman ɗaukin kare kai
Ya ce a yanzu haka gwamnatin ta duƙufa aiki da dare ba rana kan sabbin dabarun da zasu kawo ƙarshen matsalar tsaro baki ɗaya a Najeriya.
A cewarsa, majalisar koli ta tsaro ta amince da wasu sabbin dabaru domin ganin bayan matsalar, ya tabbatar da cewa za'a ƙara matsa kaimi kan ayyukan ta'addanci.
Asali: Legit.ng