Budurwa ta amince zata kwanta da saurayi, ta roke shi N15k, ya danna mata ashar tare da cewa zuciyarta ta mutu
- Wani matashi ya zabga wa budurwa ashar bayan ta nemi N15,000 da gaggawa daga wurin shi saboda ta amince za ta kwanta da shi
- Ya caccaketa inda yace tsararta ce Tobi Amusan da ta samu nasarar lashe gasar tsere har aka gwangwajeta da $100,000 a matsayin kyauta
- A sautin muryar tattaunawa da aka yi tsakanin saurayin da budurwarsa, an ji yadda ta kaskantar da kanta, lamarin da ya ja matashi ya baje ta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
A wata tattauna da aka yi ta a manhajar WhatsApp dake dauke da sautin murya na wani matashi da budurwar shi wacce ke rokon kudi, saurayin bai sassauta mata ba sai da yayi mata gori.
A tattaunawar, budurwar ta roki saurayin da ya taimaka ya turo mata N15,000 kuma ta bayyana masa cewa da gaggawa take bukatar kudin.
A martanin saurayin, ya antayawa mahaifiyar budurwar zagi kuma ya kara da bayyana yadda mai wasan tsalle Tobi Amusan ta kasance tsararta wacce ta samu nasara a rayuwa.
Ya bayyana yadda Tobi Amusan ta zabi inda ta fi kwarewa kuma har ta samu nasarar samun &100,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sautin muryar, ya caccaki budurwar har da ta tambaye shi kudi saboda ta amince zata kwanta da shi, bata duba darajarta ta nemi na kanta ba.
Yadda budurwa ta shiga bariki, bayan shekaru 6 ta koma gida da cutukan kanjamau da TB
A wani labari na daban, wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai amfani da sunan @soltune ya bayyana yadda 'yar uwar shi ta bar gida, bayan shekaru shida kuma ta dawo musu da cutukan Kanjamau da TB wanda daga bisani ta warke.
Kamar yadda Soltune yace, 'yar uwarshi ta bar gida a shekaru shida kuma bata dawo ba har sai shekarar da ta gabata yayin da wasu mutane suka kawo ta gida magashiyyan.
Ya wallafa hotunan kanwar shi a lokacin da wasu suka kawo ta gida da kuma lokacin da ta warware kamar ba ita ba a ranar 27 ga watan Yulin 2022.
"A wannan shaidar, kai tsaye zan je kan maganar abinda zan tattauna a kai, babu dogon labari. Shekaru shida da suka wuce, 'yar uwata ta tashi ta bar gida haka kawai. A cikin wadannan shekarun, na rasa mahaifina da 'yar uwata, mahaifiyata da 'yan uwana suna shan wahala amma mun cigaba da addu'a da yarda da Ubangiji," yace.
Asali: Legit.ng