Abin da ya sa Muka Zaftare Dala Biliyan 1 daga Asusun Rarar Mai inji Ministar Buhari

Abin da ya sa Muka Zaftare Dala Biliyan 1 daga Asusun Rarar Mai inji Ministar Buhari

  • An wayi gari an ji cewa Gwamnatin Tarayya ta dauki Dala Biliyan 1 daga asusun kudin rarar mai
  • Ministar kudi, Zainab Ahmed ta kare zargin da ake yi wa Gwamnatin Muhammadu Buhari
  • Ahmed tace Majaliar NEC da Gwamnonin Jihohi sun san da kudin sayen makaman da aka cire

Abuja - Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed tayi karin-haske a kan kudin da aka dauka daga asusun rarar mai na ECA.

The Cable ta rahoto Ministar tana cewa Gwamnoni da ‘yan majalisar NEC mai kula da tattalin arziki sun san da batun kudin da aka cire daga asusun.

Zainab Ahmed tayi wannan bayani ne bayan an tashi taron FEC a ranar Larabar da ta gabata.

A karshen taron FAAC da aka yi na watan Yuli, an ji labarin abin da ke cikin asusun rarar kudin mai ya ragu daga Dala miliyan $35.37 zuwa $376,655.

Kara karanta wannan

Duk sace N109bn na kasa, kotu ta ba da belin akanta janar da shugaba Buhari ya dakatar

Kwamitin na FAAC bai yi wani cikakken bayanin abin da ya jawo kudin ya ragu haka ba musamman a lokacin da ake saida gangar danyen mai da tsada.

Menene rarar mai?

ECA wani asusu ne na musamman da aka yi tanadi domin adana rarar danyen mai. Rarar na nufin bambancin abin da aka yi kasafi da farashin kasuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zainab Shamsuna
Ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmed
Asali: Facebook

A shekarar 2004 aka bude asusun da nufin gwamnatin tarayya ta boye kudi a lokacin da danyen mai ya yi tsada a Duniya, kudin za su yi rana a nan gaba.

Premium Times ta rahoto Ministar tana mai cewa Gwamnoni wanda sai da hannunsu kudi yake fita daga asusun ECA sun san an cire fam $1bn.

Zainab Ahmed tace cikin shekaru hudu da suka wuce, gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta iya adana kudi ba saboda yadda farashin mai yake yawo.

Kara karanta wannan

Darajar Naira: Bayan barazanar tsige Buhari, majalisa ta gayyaci gwamnan CBN ya ba da bahasi kan lalacewar Naira

Ministar tace babu lokacin da aka cire kudi ba tare da an sanar da ‘yan majalisar NEC ba. Kudin karshe da aka fitar $1bn ne domin magance matsalar tsaro.

An ji Ahmed tana cewa ana amfani da wannan kudi kamar yadda ya kamata. Wata majiyar tace daga cikin kudin ne aka sayo wasu jiragen ruwan na OPV.

Tsige shugaban kasa

Ku na da labari wasu Sanatocin jam’iyyar hamayya suna barazanar sauke Shugaban Najeriya a dalilin matsalar tsaro da ta adabbi bangarorin kasar nan.

A cewar Enyinnaya Abaribe, akwai Sanatoci daga APC mai rinjaye da suke goyon bayan shirin da suke yi na korar Muhammadu Buhari daga Aso Villa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng