An daidai: Martanin 'yan Najeriya bayan yankewa makashin Hanifa kisa ta hanyar rataya

An daidai: Martanin 'yan Najeriya bayan yankewa makashin Hanifa kisa ta hanyar rataya

  • Bayan yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutumin da ya kashe dalibarsa bayan sace ta, 'yan Najeriya sun yi martani
  • Da yawa daga duniyar Hausawa sun yaba da hukuncin, inda suka roka masa tsira wasu kuwa suka ce dama ya cancanci haka
  • A Najeriya akan yanke hukunci kan irin wadannan lamurra, amma akan samu tsaiko wajen zartar da hukuncin

A yau ne aka yankewa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa tahanyar rataya, watanni da kashe dalibarsa yarinya mai shekaru biyar Hanifa Abubakar bayan sace ta da neman kudin fansa.

Bayan da mahaifin jaridar ya yi martani ga hukuncin da kotu ta yanke, jama'ar Najeriya a bangarori da dama sun tofa albarkacin bakinsu.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, an sha yanke hukunci a Najeriya amma zartar dashi ya zama babban aiki ko ya zo da tasgaro.

Kara karanta wannan

An yi adalci: Mahaifin Hanifa ya yi martani bayan hukunta malamin da ya kashe masa diya

Martanin 'yan Najeriya bayan hukunta makashin Hanifa
An yi daidai: Martanin 'yan Najeriya bayan yankewa makashin Hanifa kisa ta hanyar rataya | Hoto: dailytrust.com
Asali: Instagram

A rahoton da muka hada, mun tattaro abin da mutane ke cewa game da hukuncin da kotu ta yanke na rataye Abdulmalik Tanko.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin 'yan Najeriya

Mun tattaro muku kadan daga abubuwan da 'yan Najeriya ke cewa a karkashin rahoton hukuncin kotun Kano kamar haka:

@Amina Sanda Ngamdu ta ce:

"Allah yasa ayi hukuncinda sheria taamince dashi bisa tafarkin addinin musulunci."

@Buhari Garba Doya Bauchi ya ce:

"Zantar da hukuncin cikin gaggawa zai ƙara tabbatar da izzina wa masu mummunar tunani da mungun nufi a cikin al'umma. Jinjina ga ma'aikatan Shari'a ta Najeriya. "

@Rabi'u Daura ya ce:

"Idan ta tabbata an zartar masa hukunci kisan, Allah ya amshi tubansa.
"Su kuma Iyayen yarinyar Allah ya ƙara musu haƙurin rashin ta.
"Mu kuma Allah ya kiyaye mu da mummunar ƙaddara, ya sanya ƙarshen mu ya yi kyau."

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Kotu Ta Yanke Wa Abdulmalik Tanko Da Hashimu Hukuncin Kisa Bisa Laifin Kashe Hanifa Abubakar

@Mustapha Salihu Dan Dada ya ce:
"Ba yanke Hukuncin ne Matsalar ba.Aiwatarwar shine damuwa.
"Da ana zartar da hukunci a kasar nan kan masu laifi da an samu saukin wasu Al'amuran."

@Bashir Muhammad Tagana ya ce:

"Allah muke Roqo ya kare mu daga mummunan Qaddarora
"Allah yasa muyi kyakkyawan Qarshe, Allah yasa Wannan Hukuncin ya zama kaffara gare shi,
"Allah yasa Wannan ya zama darasi ga duk masu Qoqarin Aikata irin Wannan."

@Ahmad Tilldown ya ce:

"Hukunci yayi daidai da abinda ya aikata.ammafa akwai kura kunsan ansami masu kashe rayukan Al umma dayawa kuma anyanke musu hukuncin kisa Amma an sakesu kuma to Allah ya gyara Mana kasarmu yasa daga kansa agyara hukunci ya sa mudace masu irin wannnan zuciyar sudaina sugane gaskiyadayace Al barkacin fiyayyen alitta Annabinmu S.A.W."

Mun san za a yi adalci: Mahaifan marigayiya Hanifa sun yi martani bayan hukunta malaminta

A ani labarin, bayan kai ruwa rana a kotu, an yankewa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kama shi da laifin sacewa, kashewa gami da wulakanta gawar dalibarsa Hanifa Abubakar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Buhari zai sanya takunkumi kan BBC da Aminiya saboda kambama 'yan ta'adda

Jim kadan bayan hukuncin, iyayen marigayiyar sun fito sun yi bayani, inda suka bayyana irin yanayin da suka shiga da jin hukuncin da aka yanke wa makashin diyarsu.

A wani bidiyon da jaridar Aminiya ta yada a kafar sada zumunta ta Twitter, Legit.ng Hausa ta ji irin martanin mahaifin Hanifa da ma na mahaifiyarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.