Hotuna da bidiyo: Tukur Buratai zai aurar da zukekiyar diyarsa, shagulgula sun kankama

Hotuna da bidiyo: Tukur Buratai zai aurar da zukekiyar diyarsa, shagulgula sun kankama

  • Kyawawan hotuna da bidiyoyin shagalin auren Fatima Tukur Buratai da za a yi a wannan makon sun fara bayyana
  • Tsohon shugaban rundunar sojojin kasa Na Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai zai aurar da 'ya a wannan makon
  • Tuni shagulgula suka fara kankama inda hotuna da bidiyon wurin liyafar wankan amarya suka fara fitowa

Tsohon shugaban rundunar sojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya, zai aurar da diyar sa a wannan ranakun karshen makon mai zuwa.

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta tattaro muku daga shafin @fashionseriesng na Instagram, Fatima Tukur Buratai ta fara fitar da hotunan kafin aure da yadda aka dauke su.

Fatima Buratai
Hotuna da bidiyo: Tukur Buratai zai aurar da zukekiyar diyarsa, shagulgula sun kankama. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

Daga nan, hotunan liyafar wankan amarya da suka matukar kayatarwa sun bayyana. An ga zukekiyar budurwar tare da kawayenta inda suke shagali tare da rakashewa duk don taya ta murnar wannan babban al'amarin da zai same ta.

Kara karanta wannan

Ayiriri: Sarkin Daura ya sake yin wuff da budurwa mai shekaru 22, hotuna sun bayyana

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kyawawan hotunan Hadiza Buhari cikin iyalan Malami sun kayatar, uwargida ta karbeta hannu bibbiyu

A wani labari na daban, sabbin hotunan Nana Hadiza Muhammadu Buhari a cikin iyalan ministan shari'ar Najeriya kuma antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, SAN, sun matukar kayatar da jama'a.

A kyawawan hotunan da @surrykmata ta wallafa a shafinta na Instagram, an ga sabuwar amaryar tare da mijinta, a wani hoton kuma tare da uwargidanta yayin da wani ya bayyana tana cikin iyalan.

An daura auren a Abuja yayin da aka yi karamin biki a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake Abuja tare da 'yan uwa da abokan arziki.

Daya daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Daga siriri zuwa lukuti: Bidiyo da hotunan yadda kwarewa a girkin budurwa ya canza saurayi

Asali: Legit.ng

Online view pixel