Dattijuwa Mai Shekaru 60 Ta Haifi Yan Uku Bayan Shafe Tsawon Lokaci Tana jiran Tsammani, Hotuna
- Allah ya albarkaci wata dattijuwa mai shekaru 60, Chinwe Mbahotu, da haihuwar yara har guda uku
- Mbahotu wacce ta haifi maza biyu da mace daya ta shafe tsawon lokaci tana neman haihuwa a gidan aurenta amma sai yanzu Allah ya amsa addu'anta
- Jama'a sun taya ta murnar wannan kyauta da Allah ya yi mata, yayin da suka yi mata fatan samun lafiya
Bayan tsawon shekaru da dama tana jiran tsammani, Allah ya albarkaci wata yar Najeriya mai suna Chinwe Mbahotu da haihuwar yan uku.
Mbahotu, wacce shekarunta suka haura 60 a duniya ta haifi maza biyu da mace daya.
Wani dan uwan matar, Cliff Ayozie, ne ya wallafa labarin mai dadi a shafin Facebook, inda ya bayyana cewa ta haihu ne a Dallas, kasar Amurka a cikin makon jiya.
Ya rubuta a shafin nasa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Uwa a shekaru 60+ Allah ya albarkace ta da samun yan uku. Maza biyu da mace daya a Dallas, US. Uwa da ‘ya’ya na cikin koshin lafiya. Yar uwata, Chinwe Mbahotu na ta tsammanin wannan kyauta na musamman a tsawon shekarun aurenta. Yanzu, Ubangiji ya ziyarceta don sauya shekarun bakin ciki zuwa na farin ciki da murna. Ku taya mu addu’a da farin ciki.”
Jama’a sun yi mata fatan alkhairi
Bernard Ejiogu ya yi martani:
“Allah da girma yake. Ina taya ki murna kuma Allah ya baiwa uwa da yayan lafiya.”
Evelyn Ekpen-Nwosu ta ce:
“Ubangijinmu kenan. Shekara dubu kamar kwana daya ne a wajensa.”
Okwuonu Victor ya ce:
“Wow…wannan labara ne mai dadi. Allah mun gode maka!”
Kyakkyawan Bidiyon ‘Yar Karamar Yarinya Tana Sarawa Sojoji Ya Kayatar Da Mutane
A wani labarin, wani bidiyo na wata kyakkyawar yarinya karama tana karrama wasu jami’an sojoji ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu a shafukan soshiyal midiya.
Karamar yarinyar ta gano jami’an tsaron sanye da kayan sojoji sai ta ruga da gudu zuwa wajensu. Sai ta taba kafar daya daga cikinsu sannan ta shafa goshinta da hannun nata.
Sojojin sun kalle ta cike da mamaki sannan duk suka yi mata murmushi cike da jin dadi. Sai ita murmusa kafin ta sara masu.
Asali: Legit.ng