Gogaggen Dan jarida, Mallam Abdulhamid Agaka Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Gogaggen Dan jarida, Mallam Abdulhamid Agaka Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Mallam Abdulhamid Babatunde Agaka, gogaggen dan jarida kuma kwararre a bangaren kafafen watsa labarai ya riga mu gidan gaskiya.
  • Marigayin wanda ya fara aikin jarida tun shekarar 1974 ya rasu ne cikin barcinsa bayan da ya kwanta a daren ranar Laraba a gidansa da ke Kaduna
  • Mallam Abdulhamin ya rasu ya bar yaya guda hudu da yan uwa cikinsu har da Mr Ilyasu Baba Agaka, direkta a fadar shugaban kasa

Jihar Kaduna - Gogaggen dan jarida kuma kwararre a bangaren kafar watsa labarai, Mallam Abdulhamid Agaka, ya riga mu gidan gaskiya, rahoton Leadership.

A cewar kafar watsa labarai ta PRNigeria, dan jaridar wanda matarsa da mutu a makon da ya wuce, ya mutu cikin barcinsa a daren ranar Laraba a gidansa da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

Borno: Yan Boko Haram Sun Kai Wa Tawagar Shugaban Ƙaramar Hukumar Hari, Sun Kashe Ɗan Sanda

Malam Abdulhamid Babatunde Agaka.
Gogaggen Dan jarida, Mallam Abdulhamid Agaka Ya Riga Mu Gidan Gaskiya. Hoto: @PRNigeria.
Asali: Twitter

Takaitaccen tarihin Mallam Abdulhamid

An haife shi a ranar 26 ga watan Fabrairun 1956, Malam Babatunde Agaka ya yi karatun frimare a Capital School Kaduna, kafin ya tafi Kwallejin Barewa da ke Zaria, duk a Kaduna ya kuma tafi Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Ilorin, Jihar Kwara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya fara aiki da jaridar New Nigerian, jaridar farko a arewa da ke Kaduna a shekarar 1974.

Daga baya, ya koma tsohuwar jaridar Democrat Newspaper a matsayin Edita daga 1988 zuwa 1997, sannan ya koma aikin bada shawarwari kan kafar watsa labarai.

Malam Babatunde Agaka, wanda ya hallarci tarurukan horaswa da karin ilimi masu yawa a gida da waje, mamba ne na Cibiyar aikin jarida ta Najeriya, NIJ, a Legas.

An tattaro kuma cewa ya rike mukamai a kungiyar editoci ta Najeriya, NGE, inda ya ke mamba.

Kara karanta wannan

Hotuna: Kakakin Majalisar Najeriya, Gbajabiamila Ya Koma Makaranta A Amurka

Yaya yan uwa da marigayin ya bari

Malam Babatunde Agaka, wanda ya taba rike mukamin sakatare na Kwamitin Jokolo da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya kafa a 1999, ya bar yara hudu: Ahmad, Maryam, Halima da Abdulhamid (Jnr).

Ya kuma bar yan uwa da suka hada da Mallam Ismail Ila Agaka, tsohon manajan direkta na 'Nigeria Social Infrastructure Trust Fund, NSITF, da Ilyasu Baba Agaka, direkta a fadar shugaban kasa da wasu.

Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Rikon Kwarya Na BUK Rasuwa

A wani labarin, tsohon shugaban rikon kwarya na Jami'ar Bayero ta Kano, BUK, Farfesa Danjuma Maiwada, ya rasu yana da shekaru 70 a duniya, Daily Trust ta ruwaito.

Maiwada, wanda ya yi aiki na kankanin lokaci a matsayin shugaban riko na BUK a 2004, dan asalin Jihar Katsina ne amma mafi rayuwarsa a Kano ne inda ya ke koyarwa a jami'ar tun 1976 a tsangayar ilimi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164