Kotun Kano ta Ki amincewa da bukatar mayar da Shari’ar Sheikh Abduljabbar Abuja

Kotun Kano ta Ki amincewa da bukatar mayar da Shari’ar Sheikh Abduljabbar Abuja

  • Kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta ƙi yadda da buƙatar mayar da shari’ar Malam Abduljabbar Nasir Kabara zuwa Abuja
  • Malam Abduljabar ya zargi alkalin kotun tarayya na jihar Kano da ganawa da kwamsihinan shari’a Barista Musa Lawan gabanin zaman kotun
  • Alkali Mai Sharia Abdullahi Liman ya umarci lauyan Malam Abduljabbar ya rubuto zargin da yake masa

Jihar Kano - Kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta ƙi yadda da buƙatar mayar da shari’ar Malam Abduljabbar Nasir Kabara zuwa Abuja. Rahoton BBC

Abduljabbar dai ya bukaci kotun da ta mayar da shari’ar tasa zuwa wata kotun a Abuja saboda zargin da yake na cewar kotun Kano ba za ta yi masa adalci ba.

Legit.NG ta rawaito a zaman kotun da aka yi a makon da ya gabata yadda Malam Abduljabbar ya nemi a canza masa kotu saboda zargin kotun Kano bata bashi damar kare kansa yadda ya kamata ba.

Kara karanta wannan

An Yi Jana’izar Daya Daga Cikin Sojojin Da Yan Bindiga Suka Kashe A Abuja, Hotuna

Kabara
Kotun Kano ta ƙi amincewa da buƙatar mayar da shari’ar Sheikh Abduljabbar Abuja FOTO BBC
Asali: UGC

A zaman kotun da ya gudana ƙarƙashin Mai Shari’a Abdullahi Liman a ranar Laraba 27ga watan Yuni, lauyan Abduljabbar, Barista Dalhatu Shehu Usman ya zargi alkalin kotun tarayyar na Kano da ganawa da kwamsihinan shari’an jihar Kano Barista Musa Lawan a safiyar jiya gabanin zaman kotun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakan da Alkalin yayi yasa Malam Abduljabar ya karaya inda ya ce ba a mishi adalci ba kuma ganawar kwamishina da Alkali ya saba ka’ida.

Lauyan gwamnati Barista Dahiru Muhammad, A yayin da yake mayar da martani ya ƙalubalanci batun da Abuljabar yayi.

Alkali Mai Sharia Abdullahi Liman ya umarci lauyan Malam Abduljabbar ya rubuto zargin da yake masa na zuwan Kwamishinan Shari’an jihar Kano wajen sa, tare da bayyana abin da suka tattauna.

Kotu Ta Bada belin Dakataccen Akanta-Janar

A wani labar, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Babban Akanta Janar na Tarayya, Idris Ahmed tare da wadanda ake tuhumar su bisa sharuddan da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati EFCC ta bayar. Rahoton Channels TV

Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Adeyemi Ajayi ya ba da umarnin cewa wadanda ake tuhumar ba za su bar birnin tarayya ba, kuma idan sun so sai su nemi izinin kotu ko kuma a soke belinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa