An Yi Jana’izar Daya Daga Cikin Sojojin Da Yan Bindiga Suka Kashe A Abuja, Hotuna
- An yi jana'izar daya daga cikin sojojin da yan bindiga suka kaiwa farmaki a babbar birnin tarayya Abuja
- Marigayi Laftanal Ibrahim Jauro na cikin Sojojin Bataliya ta 7 da yan bindiga suka kashe a hanyar Kubwa zuwa Bwari a ranar Lahadi
- An sada Jauro da gidansa na gaskiya bayan yan uwansa sojoji sun yi masa karramawar karshe
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
An yi janai’azar Marigayi Laftanal Ibrahim Jauro, daya daga sojojin fadar shugaban kasa da yan bindiga suka kashe a Abuja.
A ranar Lahadi ne yan bindiga suka kai wa Sojojin Bataliya ta 7 hari a hanyar Kubwa zuwa Bwari a babban birnin tarayya Abuja.
Hakazalika sojoji uku ne suka kwanta dama a yayin harin kamar yadda mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin Captain Godfrey Abakpa, ya bayyana.
Sojoji sun yiwa marigayi Jauro karramawar karshe cikin ruwan sama kafin aka sada shi da gidansa na gaskiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani dan uwan marigayin mai suna Jhamyl Jae ya je shafinsa na Facebook inda ya wallafa hotunan jana’izar tare da yiwa marigayin addu’an samun Aljannah.
Ya rubuta:
“Allah ya ji kanka a Jannatul Firdausi dan uwa.... @ LATE LT IBRAHIM JAURO.”
'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaron fadar shugaban kasa bayan barazanar sace Buhari
A baya mun kawo cewa kasa da sa'o'i 24 da 'yan ta'adda suka yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna Nasir El'Rufai a wani faifan bidiyo, wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka yi wa sojojin na Guards Brigade kwanton bauna a Abuja.
Sojoji uku ne suka jikkata yayin harin wanda ya jefa mazauna birnin tarayya Abuja cikin firgici, rahoton The Nation.
‘Yan bindigar sun nufi makarantar koyon harkokin shari’a ta Najeriya da ke Bwari a lokacin da suka ci karo da jami'an sojojin.
Asali: Legit.ng