Borno: Yan Boko Haram Sun Kai Wa Tawagar Shugaban Ƙaramar Hukuma Hari, Sun Kashe Ɗan Sanda
- Wasu yan bindiga da ake zargin yan Boko Haram ne sun kai wa jerin gwanon motocin shugaban karamar hukumar Nganzai a Borno hari
- Mohammed Bashir Bukar, hadimin shugaban karamar hukumar Nganzai, Hon Asheikh Mamman ya ce mai gidansa lafiyarsa lau kuma ba a sace shi ba
- Bukar, amma ya ce jami'in dan sanda guda daya daga cikin tawagar ya riga mu gidan gaskiya sakamakon harin da yan ta'addan suka kai musu a hanyar su ta zuwa wani aiki
Borno - Ɗan sanda ya riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai wa tawagar motocin shugaban karamar hukumar Nganzai a Jihar Borno, Hon Asheikh Mamman Gadai, hari a ranar Laraba.
Lamarin ya faru ne a hanyar Gajiram da Gajiganna lokacin da Asheikh da tawagarsa ke hanyarsu ta zuwa wani aiki, rahoton Daily Trust.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hadimin Asheikh ya tabbatar da afkuwar harin
A cikin sanarwa, Mohammed Bashir Bukar, mataimaki na musamman ga shugaban karamar hukumar Nganzai a bangaren watsa labarai ya tabbatar da harin.
Sanarwar ta ce Hon Asheikh lafiyarsa kalau, ɗan sanda cikin tawagarsa ya rasu.
An bukaci al'umma su yi watsi da jita-jitar cewa yan ta'addan sun sace Hon Asheikh.
Amma, sanarwar ba ta bada karin bayani game da harin ba. An yi kokarin ji ta bakin Bukar a lokacin hada wannan rahoton amma ba a same shi ba.
A halin yanzu dai Najeriya na fama da matsalar rashin tsaro da ake yi wa kallon mafi muni a tarihin kasar.
Dakaci karin bayani...
Asali: Legit.ng