Fadar Shugaban kasa tayi Martani Mai Zafi ga Sanatocin da ke Yunkurin tsige Buhari

Fadar Shugaban kasa tayi Martani Mai Zafi ga Sanatocin da ke Yunkurin tsige Buhari

  • Garba Shehu ya fitar da jawabi a dalilin wa’adin da wasu Sanatoci suka ba Muhammadu Buhari
  • Mai magana da yawun bakin shugaban na Najeriya ya yi wa ‘Yan Majalisar dattawan kaca-kaca

Malam Shehu yace gwamnati na kokarin kawo karshen matsalar tsaro da ta dabaibaye kasar nan

Abuja - Fadar shugaban kasa ta maida martani ga Sanatocin jam’iyyar hamayya da suke yi wa shugaba Muhammadu Buhari barazanar tunbuke shi.

Jaridar Daily Trust tace Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar da wani jawabi a ranar Alhamis, a matsayin martani.

Garba Shehu ya kuma yabi shugaban majalisar dattawa wanda ya takawa Sanatocin burki, Kakakin yake cewa Ahmad Lawan ya yi abin da ya kamata.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Buhari ya yi martani kan barazanar tsige shi da sanatocin PDP suka yi

A jawabin da ya fitar, Mai magana da yawun shugaban kasar yace Sanatocin PDP da suka fice daga majalisa saboda maganar, sun nuna halin yarinta.

Gwamnatin Buhari ta na iyakar kokari

Shehu yake cewa gwamnatin Muhammadu Buhari da gaske take yi wajen magance matsalar tsaro, har da wanda ta gada daga hannun gwamnatin PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga cikin nasarorin da aka samu a makon nan, an ceto wasu daga cikin ‘yan matan Chibok.

Shugaba Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari a Lisbon Hoto: GarShehu
Asali: Facebook

“Muna maraba da hadin-kansu wajen kokarin magance matsalolin da mutanen Najeriya ke fuskanta kullum.
“Babu wanda ya nemi su yi yunkurin tsige shugaban kasar da aka zaba, yana shirin kammala wa’adin karshe.

- Malam Garba Shehu

The Nation tace Shehu yana ganin ‘yan majalisar dattawan sun dauko dala babu gammo domin ba wadanda suke wakilta suka nemi a sauke Buhari ba.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Shugabanci Na Gari ne Kadai Maganin Juyin Mulki a Nahiyar Afrika

Bata lokaci ne - Fadar Shugaban kasa

“Sai su tambayi kansu, suna son aiki a gwamnati ne ko kuwa suna son shiga labarai ne? Idan aiki za su yi, sai su dage, su daina raina masu zabe a Najeriya.”
“A maimakon hakan, suyi koyi da Amurka, inda ‘yan adawa ke bata lokaci a tattauna muhimman batutuwa kamar tsadar rayuwar da ake fuskanta a Duniya.”

- Malam Garba Shehu

Za ayi zama a Aso Villa

'Yan awanni ke da wuya da jin Sanatoci suna maganar za a nemi a tunbuke Shugaba Muhammadu Buhari, sai muka samu labari ya kira wani taro a yau dinnan.

Shugaban kasar zai zauna da Hafsoshin sojoji da shugabannin tsaro da nufin ganin yadda za a bullowa matsalar rashin tsaro da ya yi katutu a duk fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng