Yanzu-Yanzu: An Rufe Wata Jami'ar Abuja Saboda Fargaban Harin Yan Ta'adda
- Jami'ar Veritas, mallakar cocin Katolika, da ke karamar hukumar Bwari a birnin tarayya Abuja ta rufe karatu ta umurci dalibai su tafi gida.
- Sanarwar da kakakin jami'ar, Evelyn Obekpa, ta fitar a ranar Laraba ya ce an rufe makarantar ne saboda umurnin ministan Abuja kuma an kammala zangon karatu na 2022/2022
- Jami'ar ta bayyana cewa dalibanta na aji daya ba su riga sun rubuta jarrabawa ba amma nan gaba za ta sanar da lokacin da za su rubuta
FCT, Abuja - Jami'ar Veritas da ke birnin tarayya Abuja, ta umurci dalibai su tafi gidajensu ta dakatar da karatu saboda tabarbarewar tsaro a Abuja da kewaye.
An rufe jami'ar mallakar cocin Katolika, da ke karamar hukumar Bwari a Abuja ne bayan samun rahotannin tsaro da ke nuna cewa akwai yiwuwar yan ta'adda su kawo hari tare da sace dalibai da kuma dakile harin da jami'an tsaro suka yi a makarantar koyon aikin lauya da ke kusa da jami'ar.
An dakatar da fara zangon karatu a Satumba saboda barazanar tsaron da ake fuskanta a makarantar, rahoton Vanguard.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Duk da cewa jami'ar ta Veritas, cikin sanarwar da ta fitar ranar Laraba ta ce ta kammala karatun wannan zagon hakan yasa ta rufe, Vanguard ta tattaro cewa rufewan na da alaka da barazanar da aka yi wa makarantar da hukumomin tsaro.
Sanarwar da Jami'ar Veritas ta fitar
Mai magana da yawun jami'ar ta Veritas, Evelyn Obekpa, ta tabbatar da rufe makarantar, a ranar Laraba, ta ce:
"Mahukunta Jami'ar Veritas na son sanar da mutane cewa ta kammala zangon karatu na 2021/2022.
"Amma, saboda barazanar tsaro da kuma umurni daga Ministan FCT na rufe makarantu a Abuja, za a sanar da ranar da za a rubuta jarrabawa na yan ajin farko nan gaba."
A cewar sanarwar, dalibai da ke sha'awan shiga jami'ar suna iya ziyartar shafinta na intanet domin yin rajista na zangon karatu na 2022/2023.
Yan Bindiga, Yan Ta'adda Na Shirin Kai Hari Legas, Abuja, Katsina Da Wasu Jihohi 3, In Ji NSCDC
A wani rahoton, Hukumar tsaro ta NSCDC ta umurci dukkan rundunonin ta su kasance cikin shiri bayan samun rahoton sirri da ke nuna yan Boko Haram da ISWAP suna shirin kai hari a Abuja da wasu jihohi biyar har da Legas, rahoton Vanguard.
akardar bayanan da ya fito mai dauke da kwanan watan ranar 25 ga watan Yuli mai dauke da sa hannun mataimakin kwamandan Janar, Dauda Alkali Mungadi, ga rassan rundunar NSCDC ta ce kungiyoyin yan ta'addan sun kammala shirin kai hari Abuja da wasu jihohi.
Asali: Legit.ng