Hukumar Kula Da Birnin Tarayya FCTA Ta Murkushe Babura 1,700

Hukumar Kula Da Birnin Tarayya FCTA Ta Murkushe Babura 1,700

  • Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ta murkushe babura sama da 1,700 da gwamnati ta kama
  • Tun shekarar 2006 hukumar babban birnin tarayya Abuja FCTA ta haramta hawa babura a cikin birnin tarayya
  • Kwamishinan Yansanda na Abuja ya ce wasu miyagun laifuka da wasu mutane ke aikatawa ta hanyar amfani da babura ya sa aka kara kaimi wajen kama babura a Abuja

Abuja - Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ta murkushe babura sama da 1,700 da gwamnatin ta kama, a daidai lokacin da ta haramta gudanar da ayyukan babur (Okada) a babban birnin kasar. Rahoton Leadership

Da yake jawabi ga manema labarai a yayin da aka fara atisayen murkushe Babura kashi na biyu a Wuye a ranar Larabar da ta gabata, Daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta babban birnin tarayya Abuja, Dr. Abdulateef Bello, ya ce murkushe baburan din zai zama wani mataki na hana wadanda suke saba doka.

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi: Gwamna ya maida ma'aikan da gwamnatin jiharsa ta kora daga bakin aiki

Ya bayyana cewa an gudanar da atisayen na karshe ne a watan Disamba 2021 inda aka lalata wasu Babura da dama.

bikers
Hukumar Kula Da Birnin Tarayya FCTA Ta Murkushe Babura 1,700 HOTO VANGUARD
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bikes Crushed
Hukumar Kula Da Birnin Tarayya FCTA Ta Murkushe Babura 1,700
Asali: UGC

Dr Bello ya ce kokarin aiwatar da dokar hana Okada a FCT yana haifar da sakamako mai kyau. A yau, za su fara da babura sama da 1,700, wanda aka kama daga hanun mutane masu kunnen kashi dake cigaba da aiki a inda aka hana Babura shiga a birnin.

Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Sunday Babaji, wanda ya samu wakilcin mataimakiyar kwamishiniyar ‘yan sanda, Hauwa Ibrahim, ta bayyana cewa dalilan da suka sa aka kama babura a Abuja, ya biyo bayan wasu miyagun laifuka da wasu mutane ke aikatawa, ta hanyar amfani da babura.

Hauwa ta ce suna amfani da su wajen sace jakunkuna, fashin banki, kai hare-hare a wuraren zama wanda ya zama barazana ga tsaron babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Nasarawa: Tsoron harin 'yan bindiga ya sa an garkame makarantu a jihar Nasarawa

A kan haka ne aka samu kukan da ya kai ga haramta babura a cikin birnin a shekarar 2006 da hukumar babban birnin tarayya Abuja ta yi, tun daga nan muka hada kai wajen kame Okada inji ta

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa

Online view pixel