Rashin tsaro: Mun inganta Matakan tsaro a Abuja – ‘Yan sanda
- Rundunar Yansandan Najeriya ta kara baza jami'anta a babban birnin Abuja bayan rahotannin hare-hare da aka kai wasu sassan birnin
- A daren Juma'a wasu yan bindiga suka yi wa dakarun Bataliya ta 7 Guards Brigade na rundunar tsaron shugaban kasa ta Sojojin Najeriya kwanton bauna
- Rundunar Yasanda Najeriya ta bukaci jama’a su taimaka musu da bayanan sirri domin samun nasarar dakile Mastalar tsaro da birnin Abuja ke fuskanta
Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana a ranar Talata cewa ta kara baza jami’anta a babban birnin tarayya Abuja, bayan rahotannin hare-haren da aka kai wasu sassan birnin. Rahoton Premium Times
Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Legit.NG ta samu.
Bayanin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin kai hare-hare da firgici a tsakanin mazauna birnin dangane da yiwuwar karin hare-hare daga 'yan ta'adda a babban birnin kasar.
Legit.NG ta ruwaito yadda wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka yi wa dakarun Bataliya ta 7 Guards Brigade na rundunar tsaron shugaban kasa ta Sojojin Najeriya kwanton bauna a daren Juma’a a kewayen karamar hukumar Bwari da ke Abuja.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Lamarin dai ya yi sanadiyar raunata sojoji uku tare da kashe mutane takwas.
Harin dai ya zo ne makonni kadan bayan da ‘yan ta’adda suka mamaye gidan yarin Kuje da ke Abuja inda suka sako daruruwan fursunonin ciki har da wadanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne.
Daya daga cikin ‘yan ta’addan a wani faifan bidiyo ya yi barazanar cewa kungiyarsa za ta sace shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin kasar nan.
Muyiwa Adejobi, ya bukaci Jama’a A birnin su taimaka musu da bayanan sirri domin samun nasarar dakile Mastalar tsaro da birnin ke fuskanta
Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari
An bayyana sunaye da bayanan Sojojin fadar shugaban ƙasa da yan ta'adda suka kashe
A wani lbari kuma, Abuja - Bayanan wasu daga cikin jami'an da suka rasa rayukan su lokacin da yan ta'adda suka musu kwantan ɓauna a birnin tarayya Abuja ya bayyana.
Jaridar Daily Trust ta rahoto yadda Kaftin ɗin soja da wasu sojoji biyu suka mutu sanadin harin yan ta'adda a yankin Bwari a FCT Abuja ranar Lahadi da daddare.
Asali: Legit.ng