Bidiyon kyawawan 'ya'yan Gwamna Yahaya Bello da zukekiyar matarsa a jirgin sama ya kayatar

Bidiyon kyawawan 'ya'yan Gwamna Yahaya Bello da zukekiyar matarsa a jirgin sama ya kayatar

  • Bidiyon kyawawan 'ya'yan Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi tare da zukekiyar matarsa suna shagali ya dauka idon jama'a
  • A bidiyon da ya bayyana, an ga iyalan suna murnar cikar daya daga cikin 'ya'yansa shekaru 12 a duniya a cikin jirgin sama
  • An gansu rike da kofunan lemuka yayin da suke ta taya yarinyar mai kama da gwamnan murna inda kuma suke cikin farin ciki da annashuwa

Wani bidiyon kyawawan 'ya'ya da zukekiyar matar gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya matukar daukar idon masu kallo.

A bidiyon iyalan da @fashionseriesng ta wallafa a shafinta na Instagram, an ga matar gwamnan tare da 'ya'yansu cike da tsananin farin ciki da annshuwa.

Yahaya Bello
Bidiyon kyawawan 'ya'yan Gwamna Yahaya Bello da zukekiyar matarsa ya kayatar. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

A tsokacin dake kasan bidiyon, shafin ya bayyana cewa, daya daga cikin 'ya'yan gwamnan mai suna Zarah ce ta cika shekaru 12 a duniya, lamarin da yasa mahaifiyarta da 'yan uwanta suka taru suna taya ta murna da farin ciki.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi da hotunan bikin zagayowar ranar haihuwar jaruma Maryam Yahaya a Dubai

"Iyalan Yahaya Bello suna shakatawa a cikin jirgin sama yayin da Zarah ta cika shekaru 12 da haihuwa. Barka da zagoyowar ranar haihuwar ki Zarah," wallafar tace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu shakka iyalan suna cikin farin ciki yayin da suke nuna annashuwarsu a fili a cikin jirgin sama inda suke taya Zarah murnar zagayowar ranar haihuwarta.

An gansu dauke da kofunan lemuka tare da takardu da aka rubuwa "barka da zagayowar ranar haihuwar ki Zarah".

Kyawawan hotunan Hadiza Buhari cikin iyalan Malami sun kayatar, uwargida ta karbeta hannu bibbiyu

A wani labari na daban, sabbin hotunan Nana Hadiza Muhammadu Buhari a cikin iyalan ministan shari'ar Najeriya kuma antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, SAN, sun matukar kayatar da jama'a.

A kyawawan hotunan da @surrykmata ta wallafa a shafinta na Instagram, an ga sabuwar amaryar tare da mijinta, a wani hoton kuma tare da uwargidanta yayin da wani ya bayyana tana cikin iyalan.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yadda matar aure tayi mutuwar farat daya a ƙuryar ɗakin kishiyarta

An daura auren a Abuja yayin da aka yi karamin biki a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari dake Abuja tare da 'yan uwa da abokan arziki.

Daya daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya tabbatar da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng