An Kama Mata Da Miji Saboda Lakadawa Dan Sanda 'Duka' a Legas

An Kama Mata Da Miji Saboda Lakadawa Dan Sanda 'Duka' a Legas

  • Rundunar yan sanda a jihar Legas ta kama wata da mijinta kan zarginsu da duk wani jami'in dan sanda
  • Wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta a baya-bayan nan ya nuna yadda wata mata ta rike wuyan wani dan sanda tana dukansa
  • Kakakin yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya ce an tare su saboda motarsu babu lamba ne amma matar ta far wa dan sandan da duka

Jihar Legas - An kama wasu mata da miji saboda kai wa dan sanda hari a Oluwaga, Iparaja a Legas.

Wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta, ya nuna lokacin da matar ke kaiwa dan sandan hari.

An Kama Mata Da Miji Saboda Dukan Dan Sanda
An Kama Mata Da Miji Saboda Lakadawa Dan Sanda 'Duka' a Legas. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda karuwa ta dira daga bene mai hawa 5 bayan budurwar matashi ta bayyana a otal

Vanguard ta tattaro cewa mata da mijin suna tare da jinjirinsu ne cikin wata motar kirar Marsandi mara lamba, misalin karfe 2.30 na rana.

Yan sanda uku da aka ce daga Ipaja suke suka tare su don bincike, suka bukaci sanin dalilin da yasa motar ba ta da lamba.

Daga bidiyon, matar ta ki yarda daya cikin yan sandan ya shiga gaban motar domin su tafi caji ofis.

Matar, da aka bayyana sunanta a matsayin Mrs Adebayo Ayobami, daga baya ta fito daga mota da damki wuyan sandan ta fara marinsa. Yayin da ta ke rike da dan sandan da hannunta na hagu, ta fito da jinjirin daga motar da hannun ta na dama.

An ji tana cewa, "duba jinjiri na, jinjirin na kuka." Ta mayar da jinjirin mota ta cigaba da dukkan dan sandan.

Dan sandan ya kusa fusata a yunkurinsa na hana matar dukansa amma abokin aikinsa ya rika fada masa kada ya doki matar cikin harshen yarbanci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Neja Za Ta Haramta Karuwanci, Wasu Mata Da Ke Harkar Sun Magantu

An hangi mijinta ya fito daga motar daga dayan gefen. Ya janyo hankulan mutane da suka tsaya suna kallo.

Martanin yan sanda

Kakakin yan sandan Legas, SP Banjamin Hundeyin ya ce:

"Wata fasinja Mrs Adebayo Ayobami cikin fada da mummunan yanayi ta tambayi yan sandan dalilin da yasa suka tsayar da ita da mijinta a maimakon wasu motoccin. Ta ci amsa tambayoyi. A yunkurinsa na kawo su caji ofis don kara musu tambayoyi duba da halayyar ta mai janyo zargi, ita da mijinta, Ayobami Clinton suka doki yan sanda.
"An karbi motarsu. An gurfanar da su yau (jiya) a kotu sannan an basu masauki a gidan gyaran hali na Kirikiri."

Gwamnatin Neja Za Ta Haramta Karuwanci, Wasu Mata Da Ke Harkar Sun Magantu

A wani rahoton, Gwamnatin Jihar Neja za ta haramta karuwanci a Minna babban birnin jihar a matsayin wani mataki na magance rashin tsaro, Daily Nigerian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Fuskokin Wasu Daga Cikin Mutanen Da Yan Bindiga Suka Sace A Sabon Harin Kaduna

Kaltum Rufai, Sakataren dindindin a ma'aikatar mata da ayyukan cigaba na jihar ce ta bayyana hakan cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, a Minna.

Ms Rufai ta ce gwamnati ta san da wannan lamarin mara dadi wanda ka iya zuzuta kallubalen tsaro da ake fama da shi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164