Fargabar barnar 'yan bindiga ta sa IGP ya umarci a tsaurara matakan tsaro a Abuja

Fargabar barnar 'yan bindiga ta sa IGP ya umarci a tsaurara matakan tsaro a Abuja

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta umarci jami'ai da su tsaurara tsaro a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja
  • An samu hargitsi a babban birnin tarayya tun bayan da 'yan ta'adda suka kai farmaki gidan gyaran hali na Kuje
  • 'Yan ta'adda sun yi barazanar kai hari Abuja, sun kuma ce za su sace shugaba Buhari da gwamnan Kaduna, El-Rufai

FCT, Abuja - Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya bayar da umarnin a kara tsaurara matakan tsaro a babban birnin tarayya Abuja, domin kare babban birnin kasar daga harin ‘yan ta’adda.

Mazauna birnin Abuja na cikin fargaba tun bayan mamaye gidan yarin Kuje da kungiyar ISWAP a ranar 5 ga Yuli, 2022, rahoton Daily Trust.

Fiye da fursunoni 800 da suka hada da daukacin wadanda ake zargi na Boko Haram ne suka tsere a lokacin harin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani rahoton sirri ya fallasa, 'yan ta'adda sun tara makamai za su afkawa jihar Buhari

Za a tsaurara tsaro a Abuja saboda tsoron harin 'yan bindiga
Fargabar barnar 'yan bindiga ta sa IGP ya umarci a tsaurara matakan tsaro a Abuja | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

An samu bayanan sirri da dama da aka bankado kan shirin kai hari a babban birnin kasar a makon nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bangare guda, an kai harin kwanton bauna kan sojojin rundunar tsaron fadar shugaban kasa, lamarin da ya sake dagula al'amuran mazauna babban birnin tarayya Abuja.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda, Olumuyiwa Adejobi, ya ce IGP ya umarci hukumar leken asiri ta FIB da ta hada kai da mazauna yankin domin kakkabe abokan gaba.

Ya kara da cewa kada rundunar ta sarara har sai tabbatar da an samu zaman lafiya tare da kakkabe 'yan ta'adda a birnin.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Ana yi kira ga daukacin mazauna babban birnin tarayya Abuja da su hada kai su kasance tare da 'yan sanda da sauran jami'an tsaro wajen ganin mun dakile duk wani mummunan lamari a cikin babban birnin tarayya Abuja."

Kara karanta wannan

Runduna ta yi martani kan harin 'yan bindiga suka kai kan jami'an fadar shugaban kasa

Babban magana: An gano 'yan ta'adda na tara makamai za su kai garinsu Buhari

A wani labarin, jami’an tsaron NSCDC na Najeriya sun ankarar da jama'a kan harin da aka shirya kai wa garinsu shugaban kasa Muhammadu Buhari Katsina, da kuma Legas, babban birnin tarayya, da dai sauransu.

Hukumar NSCDC ta bayyana cewa, 'yan ta'addar Boko Haram da ISWAP, daga bayanan sirrin da ta tattara, sun tattara mayakansu tare da samar da muggan makamai domin aiwatar da wannan mgun aiki.

Daga makaman da suka tanada akwai na'urorin bugo jiragen sama, manyan bindigogin yaki, da dai sauransu, suna kuma kara shirye-shiryen tunkarar jihar da shugaban kasar ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.