Kamfanin Dubai Mai Ma’aikata 61,000 Ta Karrama Dan Najeriya A Matsayin Gwarzon Wata
- Wani dan Najeriya ya kafa tarihi a wani kamfanin kasar Dubai inda aka karrama shi saboda kwazonsa
- Kamfanin, Transguard Group, ta baiwa dan Najeriya mai suna Adetunji Olusola Ajao Philip lambar yawo a matsayin gwarzon watan Yuni
- Kamar yadda ake hasashe, wani dan Najeriya ko nahiyar Afrika ta yamma bai taba lashe wannan lambar yabon ba
Yan Najeriya sun jinjinawa wani matashi, Adetunji Olusola Ajao Philip, kan daukaka sunan kasar a Dubai bayan wata karramawar da ya samu a wajen aikinsa.
An karrama Olusola a wajen aikinsa, Transguard Group, a matsayin gwarzon ma’aikaci na watan Yunin 2022.
Wani da ya san matashin da aka karrama, Hajj-Saheed Omo-Iya Kunmi wanda ya wallafa labarin a Facebook ya ce Olusola ya samu lambar yabon ne a babban ofishin kamfanin a ranar Talata, 12 ga watan Yuli.
Omo-Iya ya ce ana rade-radin cewa babu wani dan Najeriya ko dan nahiyar Afrika ta yamma da ya taba samun wannan lambar yabo a tarihin kamfanin mai ma’aikatun kimanin 61,000.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake jinjinawa Olusola, Omo-Iya ya bayyana shi a matsayin jajirtacce wanda a kullun yake mayar da hankali kan duk abun da ya yarda da shi.
“Ga duk wadanda wani abu ya taba hada su da Philip a baya, duk za ku yarda dani cewa wannan ba abun mamaki bane!
“Mutumin nan a kullun yana iya kokarin bakinsa! Shi jajirtaccen mutum ne a kan duk abun da ya yarda da shi.
“Ina tayaka murna a yau, dan uwa, Ina fatan samun karin dalilai na yin haka a gaba.
“Ina tayaka murna kan wannan nasara, dan uwa. Muna godiya da ka sa mu alfahari.”
An Karrama Yar Shekara 59 Da Ke Tuka Motar Haya Don Daukar Dawainiyar ‘Ya’yanta
A wani labarin kuma, mun ji cewa bayan fice da labarinta ya yi a yanar gizo, Gidauniyar Alice Ajisafe ta karrama Misis Onokpite Agbaduta, wacce ke aiki a matsayin direbar bas.
Labarin bajinta na wannan mata mai shekaru 59 wacce ke tuka motar haya daga wannan jiha zuwa wata ta burge mutane da dama a shafukan soshiyal midiya.
A cewarta, ta zama direbar mota ne bayan rasuwar mijinta wanda ya kwanta dama a shekarar 1991.
Asali: Legit.ng