Majalisa Wakilai Ta Yi Watsi da Kudirin Neman Hana Gwamnatin Tarayya Dakatar Da Hawa Okada
- Dan majalisa wakilai daga jihar Jigawa, Abubakar Yalleman ya gabatar da kudirin neman gwamantin tarayya ta dakatar da yunkurin hana okada aiki da take yi
- Abubakar Yalleman ya ce hana aikin Okada a Najeriya ba tare da samar da wani hanyar sufuri da zai maye gurbin su ba zai janyo matsala a kasar
- Kakakin Majalissar wakilai Idris Wase, ya roki majalissa da su baiwa gwamnati hadin kai wajen yaki da rashin tsaro
Abuja - Majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin dake neman gwamnatin tarayya dakatar da yunkurin hana Babura aiki da take kokarin yi. Rahoton Channels TV
Dan majalisa daga jihar Jigawa, Abubakar Yalleman ne ya gabatar da kudirin a ranar Talata yayin zaman majalisar a zauren majalisar dokokin a Abuja.
Ya kuma roki Majalisar da ta umarci Gwamnatin Tarayya ta takaita dokar a kananan hukumomi inda fashi da ta’addanci suka yawaita.
Dan majalisar ya ce, dakatar da okada za ta yi illa ga walwala da jin dadin al'ummar Najeriya baki daya matukar ba a samar da wata hanyar sufuri da zai maye gurbin aikin su ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan gabatar da karar, mataimakin kakakin majalisar, Idris Wase, wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya dakatar kudirin, sannan yayi watsi dashi.
Ya ce ya yaba da kudirin amma ya roki ‘yan majalisar da su baiwa bangaren zartarwa na gwamnati hadin kai wajen yaki da rashin tsaro.
Ka gaji ka koma Daura: Femi Falana ya Fadawa Shugaba Buhari
A wani labari kuma, Lauyan kare hakkin dan Adam Femi Falana ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauka haka, saboda ya gaji.
Babban Lauyan Najeriya, wanda ya yi jawabi a zanga-zangar da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta gudanar a Legas, ya koka kan yadda lamuran ‘yan Najeriya ke kara tabarbarewar wanda ya shafi fannin tattalin arziki zuwa yajin aikin ASUU.
Asali: Legit.ng