Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da jerin kasashe 10 da suka fi ci gaba a Afirka, babu Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da jerin kasashe 10 da suka fi ci gaba a Afirka, babu Najeriya

  • Najeriya, kasa mafi yawan al'umma kuma mafi karfin tattalin arziki a Afirka, abin mamaki ta bace daga jerin kasashen da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na kasashen da suka ci gaba a nahiyar
  • Jerin da ake tafiya daidai hannayen jarin mutanenta da aka fi sani da jadawalin Ci gaban Dan Adam ya bayyana wasu kananan kasashe babu Najeriya
  • Rahoton ya ce kasashen sun kasance a matsayinsu ne bisa wasu abubuwa kamar tsawon rayuwa, kyakkyawar hanyoyi, hanyoyin sadarwa na zamani, da dai sauransu

Najeriya ta bace cikin firgici daga jerin kasashen da suka fi ci gaba a nahiyar Afirka bisa rahoton na ci gaban bil'adama na HDI.

Ana auna matsayin kasashe ne ta hanyoyin da suka hada da samar da ababen more rayuwa na zamani kamar kyawawan hanyoyi, ingantacciyar wutar lantarki, ingantattun hanyoyin sadarwa da tsarin kiwon lafiya mai aiki.

Kara karanta wannan

Dillalan jakuna: 'Yan Najeriya miliyan 3 za su rasa sana'a idan aka hana yanka jakuna

Najeriya ba ta cikin jerin kasashen Afrika 10 da ke da cigba
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da jerin kasashe 10 da suka fi ci gaba a Afirka, babu Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ma'auni da ake auna HDI

Sauran ma'aunai na HDI sun hada da gwamnati mai kyau, ayyuka masu kyau, samun damar kiwon lafiya da ayyuka na zamantakewa, 'yancin rayuwa a sakata a wala, da ingantaccen tsarin ilimi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Business Insider ya ba da rahoton cewa kididdigar ci gaban bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ita ce kayan aikin da aka fi amfani da ita a duniya wajen auna matsayin ci gaban kasashe.

An tsara shirin na Majalisar Dinkin Duniya ta yadda zai auna mutane ta hanyar HDI ba kawai ci gaban tattalin arziki ba.

Ma'aunan na HDI kuma na bibiyar tsawon rayuwa, ilimi tsakanin masu manyan shekaru, samun damar hawa intanet da rashin daidaito wajen samun kudin shiga. Ma'aunin na aiki ne daga matsayi 0.00 zuwa 1.00.

Kasashen da suka zo da maki kadan a ma'aunin daga 0.00 zuwa 0.66 suna da karancin ci gaban bil'adama. Samun maki tsakanin 0.55 zuwa 0.75 yana nuna kasa mai matsakaicin ci gaban bil'adama.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Abuja yayin da aka garkame makarantar sakandare saboda tsoron harin 'yan bindiga

Kasashen da ke da maki 0.70 zuwa 0.80 suna da babban kasa na HDI, yayin da kasashe masu girman ci gaban bil'adama ke da maki tsakanin 0.80 zuwa 1.0.

An lissafo kasashen Afirka da ke da mafi yawan maki na ci gaban bil'adama, duk da cewa suna kasa sosai idan aka kwatanta da sauran kasashe masu ci gaban tattalin arziki a duniya.

Jerin kasashen Afrika 10

  1. Mauritius: 0.804.
  2. Seychelles: 0.796.
  3. Algeria: 0.748.
  4. Tunisia: 0.740.
  5. Botswana: 0.735.
  6. Libya: 0.724,
  7. South Africa: 0.709.
  8. Egypt: 0.707.
  9. Gabon: 0.703.
  10. Morocco: 0.686.

‘Yan Najeriya miliyan uku za su rasa sana'a idan Buhari ya hana yanka jakuna a Najeriya - inji dillalan jakuna

A wani labarai, wani batu mai daukar hankali ya fito daga kungiyar dillalan jakuna (DDA) a ranar Litinin 25 ga watan Yulin wannan shekarar.

Kungiyar ta koka ga yadda majalisar kasar nan ke kokarin kawo dokar haramta yanka jakuna, lamarin da a cewar kungiyar zai haifar da zaman banza.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

A cewar kungiyar sama da ayyuka miliyan uku za a rasa idan aka aiwatar da shirin haramta yanka jakuna a kasar nan, 21st Centaury Chronicle ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.