Babbar Mota Ta Murkushe Sojojin Najeriya Biyu Har Lahira a Kaduna
- Wata babbar Motar kwashe shara a Kaduna ta take Sojojin Najeriya guda biyu kuma sun mutu a kan hanyar Mando
- Wani shaida da haɗarin ya auku a gabansa ya bayyana cewa Sojojin sun bugi rami suka faɗi daga kan Babur, Motar ta bi ta kan su
- Rahoto ya nuna cewa an yi gaggawar kai Sojojin guda biyu Asibitin 44 amma aka tabbatar da cewa sun cika
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kaduna - Sojojin Najeriya guda biyu sun rasa rayuwarsu yayin da wani hatsari ya rutsa da Mashin ɗin da suke kai da wata babbar Motar kwashe shara a jihar Kaduna ranar Talata.
Wani shaidan gani da ido ya faɗa wa Leadership cewa Sojojin na kan Babur da safiyar Talata yayin da suke kan hanyar koma wa wurin aiki a makarantar Sojoji (NDA) kafin daga bisani mummunan hatsarin ya rutsa da su a Mando, jihar Kaduna.
Bayanai sun tabbatar da cewa an gaggauta ɗaukar sojojin, waɗan da ba'a faɗi sunayen su ba, zuwa babban Asibitin hukumar soji na 44, daga bisani Likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa.
A bayanin wanda abun ya faru a gabansa, ya ce sojojin sun faɗo daga kan Babur ɗin lokacin da suka bugi wani Rami a kan hanyar, ita kuma babbar Motar da ta taho a bayan su ta murƙushe su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun makarantar sojojin da ke Ƙaduna watau NDA, Manjo Bashir Jajira, ya musanta samun masaniya kan abun da ya faru, Daily Trust ta ruwaito.
Jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na ɗaya daga cikin jihohin da lamarin rashin tsaro ya yi ƙamari a Najeriya.
An kai hari Jalingo
An samu hargitsi yayin da aka kama wasu 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar 'yan kwadago da ASUU
A wani labarin na daban kuma 'Yan bindiga sun kai kazamin hari babban birnin jiha, sun sace shugaban jami'an tsaro da yan mata
Tashin hankali da tsoro ya mamaye zuƙatan mazauna Jalingo, babban birnin jihar Taraba yayin da ƙarar harbe-harbe ya karaɗe birnin lokacin da yan bindiga suka kai hari da tsakar daren Litinin.
'Yan bindigan, a rahoton da Daily Trust ta tattara, sun kashe mutum uku kuma suka yi awon gaba da shugaban dakarun tsaron Bijilanti na garin da wasu ƴan mata biyar.
Asali: Legit.ng