Sunaye Da Jiha: Buhari Ya Nada Sabbin Kwamishinonin INEC 19, Ya Tura Sunansu Majalisa Don Tabbatarwa
- Shugaba Muhammadu Buhari ya tura wa majalisa sunayen mutane 19 da ya zaba don nada su kwamishoni a hukumar INEC
- Mutane biyar daga cikinsu tsaffin kwamishinoni ne da za a sabunta nadinsu yayin da sauran guda 14 kuma sabbin nadi ne
- Kwamishinonin zaben idan an tabbatar da nadinsu za su yi aiki a jihohi da suka hada da Taraba, Kano, Sokoto, Ebonyi, Cross Rivers, Katsina ds
Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabbin kwamishinoni zabe na jihohi, RECs, a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, rahoton Leadership.
Biyo bayan hakan, Shugaba Buhari ya rubuta wasika ga majalisa domin tabbatar da nadin mutane 19 da ya zaba.
Bukatar tabbatar da nadin ga majalisar na cikin wata wasika ne mai dauke da kwanan wata na ranar 25 ga watan Yulin 2022.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaba Buhari, a cikin wasikar, ya ce bukatar neman tabbatar da wadanda ya nada din ya dace da tanade-tanaden sashi na 154(1) na Kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyara).
Ya yi bayanin cewa zaben 5 daga cikin kwamishinonin sabuntawa ne yayin da sauran 14 kuma sabbin nadi ne.
Sunayen kwamishinonin na INEC da Buhari ke so a tabbatar
Wadanda aka zaba din sun hada da:
Ibrahim Abdullahi (Adamawa – Sabuntawa); Obo O. Effanga (Cross River – Sabuntawa); Alh. Umar Ibrahim (Taraba – Sabuntawa); Dr. Agboke Mutiu Olaleke (Ogun – Sabuntawa); and Prof. Samuel E. Egwu (Kogi – Sabuntawa).
Sabbin nadi
Saura sune: Onyeka Pauline Ugochi (Imo); Prof. Muhammad Lawal Bashir (Sokoto); Prof. Ayobami Salami (Oyo); Amb. Zango Abdussamadu Abdu (Katsina); Mrs. Queen Elizabeth Agwu (Ebonyi); da Dr. Agundu Oliver Tersoo (Benue).
Sauran da za a tabbatar sun hada da: Yomere Gabriel Oritsemlebi (Delta); Prof. Yahaya Makarfi Ibrahim (Kaduna); Dr. Nura Ali (Kano); Agu Sylvia Uchenna (Enugu); Ahmed Yushau Garki (FCT); Barr. Hudu Yunusa (Bauchi); Prof. Uzochukwu Ikemefuna Chijioke (Anambra); da Mohammed B. Nura (Yobe).
Buhari Ya Rubuta Wa Majalisa Wasika, Ye Nemi A Tabbatar Da Ariwoola Matsayin Sabon CJN
A wani rahoto mai kama da wannan, Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata, ya bukaci Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin mukadashin alkalin alkalai na kasa, Mai shari'a Olukayode Ariwoola, a matsayin CJN.
Hakan na cikin wata wasika da shugaban kasar ya aike wa majalisar wacce shugabanta, Ahmad Lawan ya karanto, yayin zaman majalisar, rahoton The Punch.
Buhari ya ce ya rubuta wasikar ne bisa tanadin sashi na 1 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Asali: Legit.ng