Banza ta faɗi: Bokaye sun damfari ɗan siyasa N24m bayan yaje neman sa'ar cin zaɓe, EFCC tayi ram da su
- Hukumar EFCC ta yi ram da wasu bokaye 3 da suka dinga damfarar wani 'dan siyasa kudi har N24 miliyan a jihar Ekiti
- Kamar yadda daya daga cikin bokayen ya fada, sun karba kudin da ikirarin cewa zasu siya shanu fari, ruwan kasa da baki, raguna, zobba da turare
- Sai dai tun wuri aka bai wa wani yanki takarar kujerar, lamarin da yasa 'dan siyasan ya fusata kuma ya kai bokayen kara EFCC
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama bokaye biyu wadanda suka hada kai wurin damfarar mai neman kujerar 'dan majalisar wakilai a Ekiti, kudi har N24 miliyan.
Kamar yadda Wilson Uwujaren, mai magana ga yawun EFCC ya fitar, hukumar tace Abiodun da Wale Adifala, tare da Ifawole Ajibola wanda aka fi sani da Baba Kalifa wanda ya tsere har yanzu ba a kama shi ba, sun shiga hannun hukumar ta jihar Legas a ranar 7 ga watan Yuli.
Hukumar tace su ukun sun hada kai wurin damfarar 'dan siyasan N24,071,000 wanda suka yi ikirarin zasu yi amfani da shi wurin bokancinsu domin cikar burinsa.
Kamar yadda EFCC tace, a cikin bincikenta, Adifala ya bayyana cewa ya karba kudin wanda ya hada da N2.9 miliyan wanda yayi ikirarin zai siya bakar sanuwa, ruwan kasa da fara, raguna, turare da zobba daga cikin abubuwan da ake bukata domin aikin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na kara hada lamarin da Ifawole Ajibola kuma mun cigaba da amshe kudadensa har zuwa lokacin da EFCC ta kama mu," yace.
Hukumar tace Ibrahim wanda yake da alaka da 'dan siyasan ya tabbatar da cewa ya karba kudade a lokutan daban-daban.
"Aikinmu shine yin addu'a da sauran yanka wanda muke yi kuma mun bar wa Ubangiji sauran. Ana tsaka da haka ne aka sauya yankin da za a bai wa kujerar majalisar wakilan daga Oye-Ekiti zuwa Ikole-Ekiti," yace.
Hukumar EFCC tace sun yi kamen ne sakamakon korafin da aka aike musu da shi bayan bokayen sun karbe kudin, kuma 'dan siyasan ya so karbar kudinsa amma abun ya ci tura.
Malamin addini: APC ba za ta je ko ina ba a 2023 tun da Tinubu ya zabi Musulmi abokin gami
A wani labari na daban, wani malami mai tsanain tsaurin kishin addinin Kirista Rt. Rabaran Olusola Akanbi, a karshen mako ya ce mabiya addinin kirista a kasar nan ba za su goyi bayan tikitin musulmi da musulmi na jam’iyyar APC a zabe mai zuwa ba.
A cewarsa, irin wannan matakin ya sabawa hadin kai, zaman lafiya da ci gaban al’ummar kasar nan, rahoton jaridar This Day.
Da yake jawabi a wajen taron 2022 karo na 2 na SYNOD na Diocese a Offa a jihar Kwara, Akanbi ya bayyana cewa, lamarin na jam’iyyar APC mai mulki ba zai kai jam’iyyar a ko’ina ba a fagen zabe a tsarin lissafin siyasa.
Asali: Legit.ng