KAI TSAYE: Yadda Zanga-Zangar kara ga ASUU Ke Gudana a Fadin Tarayya

KAI TSAYE: Yadda Zanga-Zangar kara ga ASUU Ke Gudana a Fadin Tarayya

A yau ranar Talata, 26 ga watan Yulin 2022, Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta fito kwanta da kwartata a titunan jihohin kasar nan domin zanga-zangar kara ga Kungiyar Malamai masu koyarwa na jami'o'in Najeriya ASUU.

Malamn jami'o'in Najeriya sun shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 kuma har yanzu babu ranar karshenta.

Legit za ta kawo muku bayanai kai tsaye kan yadda zanga-zangar ke gudana.

Ya kamata a biyawa ASUU bukatar ta, kungiyar kwadago ta jihar Ebonyi ga FG

Ma’aikata a karkashin kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Ebonyi, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta biyawa malaman ASUU bukatunsu.
Da yake jawabi a yayin zanga-zangar nuna goyon baya ga ASUU da aka yi, shugaban NLC a jihar, Mista Ikechukwu Nwafor ya ce:
“Ya kamata a cikawa ASUU bukatunsu. A kula da jin dadin ma’aikata a jami’o’i. ya kamata a mutunta yancin ma’aikata sannan a bari yaranmu su koma makaranta.
“Wannan fafutuka don ra’ayin yaranmu ne.”

Babban Lauya a Najeriya ya shiga zanga-zangar NLC a Legas

Babban lauya a Najeriya, Femi Falana (SAN) ya shiga cikin mambobin ƙungiyar kwadugo NLC a Legas, waɗan da ke gudanar da zanga-zanga don kawo ƙarshen yajin aikin ASUU.

An gudanar da zanga-zangar goyon bayan ASUU a Katsina

Kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Katsina ta bi sahun sauran takwarorinta wajen gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga malaman ASUU da ke yajin aiki.

Da yake jawabi, jagoran zanga-zangar ya ce za su gudanar da tattakin ne cikin tsari, yana mai cewa ba za su haddasa hargitsi ba domin basu da wata jaha da ta fi Katsina.

Masu zanga-zanga sun mamaye ofishin gwamnan jihar Lagas

Masu zanga-zanga sun mamaye ofishin gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu da ke Alausa kan ci tsawaita yajin aikin kungiyar malaman jami’a ta ASUU.

Zanga-zangar wanda aka fara tun daga karkashin gadar Ikeja, ya tara daruruwan mutane daga kungiyoyi daban-daban.

Masu zanga-zangar sun yi tattaki tun daga babban hanyar Ikeja har zuwa ofishin gwamnan. Lamarin ya haddasa cunkoson ababen hawa a yankin.

Hukumar NLC ta Kaduna ta fito zanga-zangar goyon bayan ASUU, Hotuna da Bidiyo

Mambobin hukumar Kwadaga, NLC, reshen Jihar Kaduna ta fito zanga-zanga domin nuna goyon bayan kungiyar malaman jami'a ta Najeriya, ASUU.

Wasu jihohi da dama suma sun fito yin zanga-zangar.

NLC ta ba Buhari wa'adin mako biyu

Ƙungiyar kwadugo ta ƙasa NLC reshen jihar Legas ta ba gwamnatin tarayya wa'adin mako biyu ta kawo karshen yajin aikin Malaman jami'o'i ASUU.

Da take jawabi a wurin zanga-zangar nuna ana tare a Ikeja, babban birnin Legas, Shugabar NLC, Misis Agnes Sessy, ta roki FG ta ɗauki mataki ko kuma ta fuskanci wata zanga-zangar #EndSARS.

Ƙungiyar NLC da wasu ƙungiyoyin jami'o'i sun fantsama kan tituna a Legas domin zanga-zanga kan yajin aikin ASUU ranar Alhamis.

Shugabar NLC a Legas ta ce:

"Idan gwamnatin tarayya ba ta shawo kan yajin aikin ASUU cikin makonni biyu ba, za'a samu ɓarkewar zanga-zanga a baki ɗaya sassan ƙasar nan, in takaice muku, zanga-zangar #ENDSARS zata zama kamar wasan yara."

Bidiyo: Kungiyar Kwadago ta Jigawa da ta dalibai sun shiga zanga-zangar taya ASUU nuna fushi

Mambobin kungiyar kwadago reshen jihar Jigawa sun bi sahun takwarorinsu na sauran jihohi wajen shiga yajin zanga-zangar lumana don nuna goyon bayansu ga kungiyar malaman ASUU.

Hakazalika, shugabannin kungiyar dalibai da kungiyoyin fararen hula a jihar sun bi sahunsu inda suka yi tattaki a garin Dutse, babbar birnin jihar ta Jigawa.

Kungiyar Kwadago ta Osun ya fito kwai da kwarkwata domin shiga zanga-zangar taya ASUU nuna fushi

Mambobin kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Ogun sun fito zanga-zangar lumana a Abeokuta domin nuna goyon bayansu ga kungiyar malaman jami'o'i.

Jihohi da yawa ne suka shiga wannan zanga-zangar hadin gwiwa da kungiyar malaman jami'o'i da ke yajin aiki watanni sama da hudu.

Kungiyar Kwadago a Gombe ta shiga sahu a zanga-zangar lumana ta hain gwiwa da ASUU

Wani bidiyo da ya yadu a kafar sada zumunta ya nuna lokacin da mambobin kungiyar NLC suka fito kwai da kwarkwata domin taya ASUU zanga-zangar lumana a birnin Gombe ta Arewa maso Gabas.

Ma'aikata sun taru a gaban ofishin NLC a Port Harcourt

Ma'aikata suna taruwa a kan titin Igboukwu, D-Line, Port Harcourt, kusa da ofishin kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC da a yanzu yan sandan Najeriya suke rufe.

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng